Bello Hamza" />

Zaben Kananan Hukumomi: APC Ta Kama Hanyar Lashe Dukkan Kujeru A Kano

APC

Daga dukkan alamu jam’iyya mai mulki na APC ta kamo hanyar lashe dukkan kujerun kananan hukumomin jihar Kano 44 da kuma dukkan kasilolinsu gaba daya, rahotannin daga runfunan zaben da aka gudanar jiya Asabar 16 ga watan Janairu yana nuna cewa, duk da an samu karancin masu jefa kuri’a, jami’iyyar APC ce ke kan gaba a kusan dukkan runfunan zaben da wakilimu ya zagaya haka kuma rahoton yake fitowa daga sauran kananan hukumokin jihar, bayani ya kuma nuna cewa, an gudanar da zabbukan cikin kwanciyar hankali ba tare wani gaggarumin rikici ba.

Wuraren da wakilinmu ya ziyarta sun hada da Chedi, Zage, Zango, Gandu, Sharada, Wailawa, Dorayi, Kabuga, Rijiyar Zaki a karamar hukumar Kano Municipal, Gwale, da kuma karamar hukumar Ungogo.

An dai fara zaben ne a daidai karfe 10:30 kamar yadda aka shirya are da kasancewa, jami’an tsaron.

Wasu da wakilinmu ya tattauana da su sun nuna jin dadin su akan yadda suka ga ake gudanar da zaben ba tare da tashin hankali ba sun kuma yada wa hukumar zaben akan yadda ta horas da ma’aikatan, don kuwa suna gudamar da ayyukan su ne ciki ne kwarewa.

Jami’iyyu 12 ne su ke takarar kujerar shugabancin kananan hukumomi 44 da kuma na kansila 484 kamar yadda shugaban hukumar zaben KANSIEC ya bayyana.

Hukumar ta kuma samar da ma’aikata 48,000 da za su yi aiki a runfunar zabe 11,500.

Haka kuma babban jojiin jihar Kano, Maishari’a Nura Sagir, ya kafa kotuna biyu da za su karbi kofa-korafe da za su fito daga zaben da aka gudanar.

Bayanin haka na kunshe ne a takarar sanarwa da jami’in watsa labarai nan ma’aikatar shari’ar, Mr Baba Jibo-Ibrahim, ya sanya wa hannun aka kuma raba wa manema labarai a Kano ranar Asabar.

“Kamar yadda ya ke a sashina 36(1) na dokokn zabe na jihar Kano na shekarar 2002, kotu nan za su saurari tare da yanke hukunci kan zabukkan da ke gudanarwa a yau Asabar,” inji shi. Ya kuma kara da cewa, sauran bayanai akan kotunan na zuwa a nan gaba.

Exit mobile version