Khalid Idris Doya" />

Zaben Kananan Hukumomi: Yadda Wasu Jihohi Su Ka Yi Wa Hukuncin Kotun Koli Kunnen Kashi

Jihar Oyo da wasu jihohi guda 12 da suke fadin kasar nan, har yanzu suna kan gudanuwa ba tare da yin zaben shugabannin kananan hukumomi ba; duk kuwa da cewar Kotun Koli ta hanasu yin hakan tsawon shekaru hudu da suka gabata.

Wani binciken da jaridar THISDAY ta yi, ta gano jihohin suna amfani ne da shugabannin riko a kananan hukumomin wadanda gwamnonin jihohin ke nadawa da juyasu ta yanda suke so a lokacin da suka so tunbukesu ma suna da ikon yin hakan.

Daga cikin jihohin da suka gaza yin zaben akwai Borno da Yobe, wadanda suke tsananin fama da rigingimun da matsalolin Boko Haram su ma sun kasa yin zaben kananan hukumomin.

Kodayake, jihohin biyun da suka kasa yin zaben kananan hukumomin tun daga shekarar 2014, sun samu damar shiga a dama da su a babban zaben 2015 da na 2019 wadanda aka samu cinciridun fitowar masu kada kuri’arsu duk da matsalar tsaro a yankin.

A hukuncin da kotun kolin ta yanke a ranar 9 ga watan Disamban 2016, ta karyata dokar da majalisun dokokin jihohi suke tutiya da shi wanda suka baiwa gwamnoni damar sauke zababbun shugabannin kananan hukumomi gami da nada shugabannin riko.

A cikin hukuncin da Kotun mai Alkalai biyar ta yanke, ta ce korar zababbun shugabannin kananan hukumomin a matsayin ‘rashin aiwatar da aiki’ da kotun ta nemi a daina hakan.

Hukuncin kotun mai Alkalai biyar a karkashin jagorancin Justice Olabode Rhodes-bibours, kotun ta bada umurnin ne a lokacin da take hukunci kan shugabannin kananan hukumomi 16 na jihar Ekiti a zamanin mulkin gwamna Kayode Fayemi a wa’adinsa ta farko.

Koton koli ta kasa da take wofintar da hamzari da Fayemi ya gabatar na rushe kananan hukumomi a jihar Ekiti, ta ce sashi na 23 (b) na dokar kananan hukumomi ta jihar Ekiti ta shekara ta 2001 wacce ta bashi damar yin hakan kan jami’an kananan hukumomi da basu gama wa’adin su ba; ta yi banbarakwai da sashi na 7 (1) na Kundin Mulkin kasa, kuma wannan doka ce, Majalisar Dokokin ta jihar Ekiti take yin tutiya da shi wajen gudanar da aiyukan ta.

Mai shara’a Centus Nweze wanda shine ya gabatar da hukuncin, ya jaddada cewar, babu yadda za a share wa’adin kananan hukumomi, ba tare raunana wasu manyan sassa na tsarin mulkin kasar ba.

Wannan hukunci ya biyo bayan wani cece-kuce ne na saukar da jami’an kananan hukumomi ba bisa ka’ida ba, kamar yadda yake faruwa a halin yanzu a jihar Oyo karkashin Jagoranci Gwamna Seyi Making.

Cece-kuce da wannan tsari na Gwamna Makinde ya kawo, ita ce tasanya tsoma hannun Ministan Shari’a na kasa, Mista Abubakar Malami (SAN), wanda ya umarci gwamnan da ya dawo da jami’an kananan hukumomi da ya rusa wa’adin su, domin biyayya ga hukunci kotun Koli ta kasa.

Malami, a cikin wata wasika da ya rubuta ranar 14 ga watan Janairu na wannan Shekara ta 2020, ya shaidawa gwamnan cewar, dangane da hukuncin kotun Koli wadda yake da tasiri akan dukkan jihohi 36 nakasar nan, rushe zabbabbun shugabannin na kananan hukumomi da gwamnoni jihohi suke yi ya sabawa Dokokin gudanar da mulkin kasa, ba shi da halacci, kuma abin kyama ne.

Babban Sifeton ‘Yan sanda na kasa, Mr. Mohammed Adamu shi ma ya umarci Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Oyo, Mr. Shine Olukolu da ya tabbatar da dawowar rusassun shugabannin kananan hukumomi, hadi kansuloli kan mulkin su.

Adamu, a cikin wata wasika da ya rubuta ranar 23rd ga watan Janairu, 2020 wa shugaban jam’iyyar APC na jihar Oyo, Chief Akin Oke, ya umarce shi da ya hada hannu da Olukolu domin aiwatar da hukuncin kotun Koli ta kasa, duk da cewar, wasu manyan lauyoyin kasar nan (SANs) sun yi hannun riga kan ta yadda za a aiwatar da hukuncin kotu.

Wasu manyan lauyoyin (SANs) kamar su Chief Mike Ozekhome, Mr. Dayo Akinlaja da Mr. John Baiyeshea sun tafi a kan cewar, ya zama a tuntubi kotun dangane da wanzar hukuncin ta, amma wasu kamar tsohon shugaban Lauyoyi ta kasa (NBA), Mr.Olisa Agbakoba da Mr. Ahmed Raji sun roki Gwamnatin Tarayya da ta rike kudaden kaso na wata-wata na tarayya na kananan hukumomi dake jihohi da hukuncin kotun Koli ya shafa, tare ajiye wadannan kudade a wani asusu na musamman, har zuwa lokacin da jihohin za su gudanar da zabenshugabannin kananan hukumomi.

Mataimakin Shugaban kungiyoyin kananan hukumomi na kasa (ALGON), Hon. Lawrence Onuchukeu ya shaida a makon da ya gabata cewar, gwamnoni suna amfani da haram-tattun jami’an kananan hukumomi ne matsayin wata rariya na kwasar kudaden jama’a dake rabawa kananan hukumomin.

Amma binciken jaridar ya nuna cewar, wannan tabargaza da ake yi na rushe zababbun shugabannin kananan hukumomi, ba yana da alaka da jihar Oyo bace kadai, domin akwai wasu jihohi goma sha biyu (12) da suka dauki wannan tsari na wofintar da hukuncin kotun koli na yin biris da umurnin yin zaben shugabannin kananan hukumomin jihohinsu.

Banda ma jihar Oyo, sauran jihohi 12 da ake yin misali wajen aikata wannan  tabargaza sun hada da Katsina, Borno, Yobe, Kwara, Kogi, Bauchi, Taraba, Benue, Enugu, Anambra, Imo da Ogun.

A jihar Ktsina, Gwamna Aminu Bello Masari ya danganta kasawar Gwamnatin jihohi gudanar da zaben kananan hukumomi ga kara da jam’iyyar PDP a jihar Katsina ta shigar a kotu dake kalubalantar rushen zababbun jami’an kananan hukumomi.

Masari, dai, idan za’a iya tunawa a shekara ta 2015 ya rushe zababbun shugabanni 34 da kamsuloli guda 361 na kananan hukumomin jihar Katsina, wadanda jam’iyyar PDP karkashin tsohon Gwamna, Alhaji Ibrahim Shema ta gudanar da zaben su.

Rushe wadannan zababbun jami’an kananan hukumomi ya sa Gwamna Amina Masari ya kafa haram-tattun jami’ai a kananan hukumomi dake jihar Katsina, wadanda galibansu, kututan ‘yan siyasa ne.

Wannan ya sanya jam’iyyar PDP ta dambara Gwamna Masari da jam’iyyar sa kara a gaban kotu. Yanzu haka wannan kara yana nan gaban Kotun Koli ta kasa.

Yayin da yake rushe zababban shugabannin a jihar Katsina a wancan lokaci, Gwamna Masari ya bayyana cewar, gwamnatinsa ba ta karya wata doka ba dangane da rushe jami’an ba, domin kamar yadda yake cewa, gwamnatinsa ta yi koyi ne da magabaciya ta jam’iyyar PDP a matakin jihar.

A jihar Anambra, akwai kananan hukumomi 21 da aee  gudanarwa ta hanyar jami’an riko a matsayin shugabannin kananan hukumomin wadanda.

Da jaridar ta tuntubi, Kwamishinan watsa labarai da fadakarwa na jihar, Mr. C. Don Adinuba ya danganta gazawar gwamnatin jihar na gudanar da zaben kananan hukumomi ga kararraki kan hakan da aka gabatar wa kotuna.

Kamar yadda ya zayyana, wata jam’iyyar siyasa ta gurfanar da gwamnatin jihar a gaban kotu kan kafa Kwamitocin riko a kananan hikimomin jihar, kazalika babban kotun jiha da babban mai shari’a kejagoranci, yayi hukuncin da yayiwa jam’iyyar dadi, Mai zummar a gudanar da zaben a kananan hukumomi.

Ya ci gaba da cewar, yanzu haka lamarin yana gaban kotun Koli  ta kasa.

A can jihar Kwara, Gwamna Abdulrahman Abdulrasak, makonni kadan da hawa karagar mulkinsa ranar 29 ga watan Mayu a shekara ta 2019, ya bayar da umarnin dakatar zababbun shugabanni na kananan hukumomi 16 dake jihar ta Kwara na tsawon watanni shida.

Daga bisani ya tsawaita dakatarwar shugannin kananan hukumomin wadanda aka zabe su a karkkashin tutar jam’iyyar PDP na mulkin tsohon Gwamna, Abdilfatah Ahmed, zuwa har illa Masha-Allahu, biyo bayan wani kudiri da Majalisar Dokokin jiha ta amincewa, wanda ya zargi shugabannin kananan hukumomin da almundahanan kudade.

Sakataren watsa labarai na gwamnan, Mr. Rafi’u Ajakaye ya ce an kara wa’adin dakatarwa na shugabannin kananan hukumomin ne biyo bayan zargin su da yin al’mundahana, sai inda binciken hukumar yaki da ta’annati (EFCC).

A jihar Taraba kuwa, zaben shiga shugabancin kananan hukumomi an  gudanar da shi ne ranar 21st ga watan Fabrairu na shekara ta 2017, aka kuma rantsar da shugabannin ranar 28th ga watan Fabrairu na wa’adin shekaru biyu.

Amma tun karewar wa’adin su ranar 28th ga watan Fabrairu na shekara ta 2019, harwa yau gudanar kananan hukumomin ne karkashin Jagorancin haram-tattun shugabanni wadanda gwamnatin jihar ta nada su.

Da yake gabatar da hujja na jinkirta zaben kananan hukumomi a jihar, Mataimaki wa Gwamna kan lamuran watsa labarai, Mr. Bala Dan Abu ya ce kafin ‘yan kwanakin nan, akwai matsanancin kalubalen tsaro a jihar ta Taraba, wanda ya hana yin zabe a kananan hukimomin jihar.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Danjuma Adamu ya bayyana cewar, gwamnatin jihar tana cikin shirye-shiryen gudanar da zabe a kananan hukumomi.

A jihar Borno kuwa, zabe da aka yi shi na karshe, an gudanar da shi ne a kananan hukumomi 27 a shekara ta 2014.

Gwamnatin jihar a kowane lokaci take gabatar da kalubalen tsaro a hujja na rashin gudanar da zabe a kananan hukumomi.

Amma duk da wannan kalubale na kurarin rashin tsaro, jihar ta shiga an dama da ita a zaben gama-gari na kasa na shekara ta 2015, dana Shekara ta 2019.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Mr. Babakura Jatto ya ki cewa uffan da manema labaru suka tuntube shi.

Jihar Yobe ma dai kananan hukumomi 17 ta bi shahu na rashin  zababbun shugabannin kananan hukumomi, wacce ita ma ta lakanta rashin zabe a kananan hukumomi wa rashin tsaro.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Abdullahi Bego, ya ki amsa sakon karta-kwana da aka tura masa a email dinsa da kuma wayarsa.

Sai dai a jihar Adamawa, wacce tana daga cikin jihohin da matsalar tsaro a shiyyar arewa maso gabas ta shafa, jihar ta gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomi 21 na jihar a watan Disamban 2019.

Wakilin LEADERSHIP A YAU ya shaido cewar a jihar Bauchi gwamnatin ta sha alwashin yin zaben kananan hukumomi nan da wata shida, jihar tana amfani da shugabanin riko ne tun bayan zaben da yi a mulkin Isa Yuguda ba a sake yin zaben a jihar ba.

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Muhammad ya sha alwashin gudanar da zaben shugabannin karanan hukumomi nan da wata shida masu zuwa domin basu dama da cikakken ikon samun ribar demokradiyya kai tsaye.

Ya shaida hakan ne a wajen walimar ta ya shi murnar samun nasara a kotun koli kan zaben jihar, ya bayyana cewar yin zaben zai taimaka sosai wa talakawa, a fadin shi jihar ta jima ba ta aiwatar da zaben shugabannin kananan hukumomi ba; sai ya bayar da tabbacin cewar shi zai yi zaben cikin farashi mai rahusa ba tare da bari an tsula maguden kudade don aiwatar da zaben ba.

A cewar shi; “A cikin wannan watar za mu bayar da sanarwar wa hukumar zabe (INEC) cewar nan da wata uku muna son mu yi zaben shugabannin karananan hukumomi.

“Tun zamanin Isa Yuguda ba a sake yin zabe ba, tun 2007 nine na yi Chairman muka yizaben kananan hukumomi tun daga wannan lokacin jihar Bauchi ba ta sake yi ba.

“Zan yi kokari a cikin wannan shekarar na yi zaben kananan hukumomi; nan da wata hudu zuwa shida za mu gudanar da zaben, domin  kowani talaka ya samu yin zabinsa,”

“Za mu gudanar da zaben cikin kankanin kudi, ba zamu yi ta yanda aka saba na kwasar maguden kudade wurin gudanar da zaben ba; ba za mu lalata dukiyar jama’an jihar hakan kan zaben ba,” Ya ce, an yi zabukan a wasu jihohi cikin kankanin farashi don haka za su bi wadannan hanyoyin don a yi hakan ma a jihar Bauchi.

A Imo kuwa: Zaben shiga shugabancin kananan hukumomi 21 da aka yi a jihar Imo an gudanar da shi ne a shekara ta 2018 karkashin jagorancin tsohon Gwamna, Rochas Okorocha.

Jaridar ta habarto cewar, Okorocha ya sauke dukkan shugabannin kananan hukumomi, wadanda aka gudanar da zaben su karkashin mulkin Chief Ikedi Ohakim, kuma ba’a gudanar da zabe a kananan hukumomi ba, sai shekara ta 2018, lokacin ya rage Shekara daya tak cikin takwas na wa’adin wancan gwamnati.

Amma, Emeka Ihedioha, kafin kotun Koli ta sauke shi matsayin da na Gwamna a kwanakin baya, ya sauke dukkan zababbun shugabanni na kananan hukumomi na jihar. Wanda ya gaje shi, Senator Hope Uzodinma, yayi alkawarin gudanar da zaben kananan hukumomi na jihar nan bada dadewa ba.

A jihar Ogun kuwa, Gwamna Dapo Abiodun yana tafiyar da lamuran kananan hukumomi da ragamar nadaddun shugabanni, yana mai cewar, zababbun shugabannin wa’adin su ya shige da watanni biyar da suka gabata.

Sakataren watsa labarai sa,  Mr. Kunle Somorin, ya shaidawa jaridar cewar, babu wani abu na muzantawa da ake nufi na sanya nadaddun shugabanni a kananan hukumomin jihar, domin zababbun shugabannin kananan hukumomin sun gama wa’adin sune a watan Oktoba da ya gabata.

“Tsare-tsaren canjin hannun mulki ne yake gudana, kuma za a gudanar zaben kananan hukumomi nan bada jimawa ba.”

“Ba a kafa hukumar zabe ta jihar ba, da zarar aka kai ga fitarwa za a tabbatar da tsara zaben shugabannin kananan hukumomin jihar,” A cewar shi.

A jihar Benue kuwa, gwamnatin da ta gabata ta yi zaben shugabbanin kananan hukumomin a watan June na shekarar 2017, wa’adinsu ya kare na tsawon shekaru biyu a watan July na shekarar 2019.

Tun daga wancan lokacin, kananan hukumomin jihar suna tafiya ne a karkashin riko da gwamnan jihar ya nada.

Kodayake, shugaban hukumar zabe na jihar Benue, (BESIEC), Mr. Tersoo Loko, ya shaida cewar suna kan tsare-tsaren aiwatar da zaben da ke cike da gaskiya da adalci.

Gwamnan jihar, Samuel Ortom ya shaida cewar BESIEC ta tabbatar mana ta shirya domin gudanar da zaben nan da watan Maris.

A jihar Enugu kuwa, zabbaben kananan hukumomin dai wa’adinsu ya kare ne tun a 3 ga watan Disamban 2019, tun daga nan ba a sake yin zaben ba.

Gwamnan jihar Ifeanyi Ugwuanyi tun daga lokacin ya nada shugabannin riko na kananan hukumomi 17 da suke jihar da yunkurin yin zaben a 29 ga watan Fabrairu.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Mr. Chidi Aroh, ya shaida cewar gwamnatin jihar ta samar wa hukumar zabe ta jihar (ENSIEC) ababen bukata da niyyar su gudanar da zaben kwanan nan.

A jihar Kogi kuwa, shugabanin kananan hukumomi 21 na nadi ne tun daga 2016, har zuwa yanzu babu wani yunkuri ko shirin aiwatar da sabon zaben shugabannin kanana hukumomin daga wajen gwamna Yahaya Bello.

Exit mobile version