Abdullahi Muhammad Sheka">

Zaben Kananan Hukumomi: Za Mu Tabbatar Da Hadin Kan Al’ummarmu – Sarkin Gaya

Mai Martaba Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim Abdulkadir, ya tabbatarwa da hukumar zabe mai zaman kanta ta Jihar Kano (KANSEIK) samun goyon bayan masarautar ta Gaya domin samun nasarar gudanar da zabe a cikin nasara.

Mai martaba sarkin na Gaya Alhaji Ibrahim Abdulkadir wanda Makaman Gaya Hakimin Albasu AIG Bashir Abdullahi Albasu mai murabus ya wakilta ne ya bayyana haka alokacin da ya karbi bakuncin tawagar Hukumar zabe mai zaman kanta ta Jihar Kano karkashin jagorancin shugaban Hukumar Farfesa Garba Ibrahim Sheka ranar Litinin a fadarsa.

Hukumar zaben mai zaman kanta ta ziyarci masarautar ta Gaya a zagayen data ke domin fadakar da shugabannin jam’iyyun siyasa a daukacin kananan Hukumomin dake masarautar a shirye shiryen zaben 16 ga watan Janairun shekara ta 2021 mai zuwa. Kamar yadda jami’in yada labaran Hukumar ta KANSEIK Dahiru Lawan Kofar Wambai ya shaidawa LEADERSHIP A YAU.

“Sarkin ya tabbatar da cewa masarautar ta Gaya zata umarci dagatai da masu unguwanni domin jan hankulan al’umma don ganin an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali kamar yadda ka’idojin zaben suka nuna, haka kuma ya jadadda fatan da suke dashi ga jagorancin wannan hukuma na ganin an gudanar da sahihin zabe a Jihar Kano,”

Da yake gabatar da jawabinsa, shugaban Hukumar zaben mai zaman kanta ta Jihar Kano Farfesa Garba Ibrahim Sheka ya bayyana cewa sunzo fadar sarkin ne domin neman sa albarkarsa tare da sanar dashi shirye shiryen zaben kananan Hukumomin dake fatan gudanarwa a shekara mai zuwa.

“Taron fadakarwar da aka gudanar a dakin taron cibiyar harkoki shari’a da ke Gaya, Kwamishinan Hukumar Zaben mai zaman kanta mai lura da harkokin jam’iyyu, Alhaji Isma’ila Rimin Gado cewa ya yi, hukumar ta yanke shawarar shigar da shugabannin jam’iyyun siyasa tun daga kasa domin ci gaba da sanar dasu dukkanin shirye shirye domin samun nasarar da ake fata.”

Da yake gabatar da jawabinsa kafin gabatar da tambayoyi da amsa, shugaban Hukumar zaben Farfesa Garba Ibrahim Sheka cewa ya yi, hukumar ta tsara zagayen masarautu biyar na Jihar Kano tare da gudanar da tattaunawa da ‘yan siyasa a matakan kananan Hukumomi domin fahimtar dasu bukatar yin duk abin da ya dace domin samun nasarar zaben.”

Madadin kananan Hukumomi tara na masarautar ta Gaya, Alhaji Ahmad Abdullahi ya godewa Hukumar zaben mai zaman kanta ya yi bisa shirya wannan taron tattaunawa inda ya tabbatarwa da Hukumar zaben cikakken goyon bayansu a wannan tsari.

Exit mobile version