Connect with us

SIYASA

Zaben Kananan Hukumomin Jihar Kaduna:Za Mu Hadu Da APC Ne A Kotu, Inji Shugaban PDP Na Jihar Kaduna

Published

on

A ranar Juma’a ne Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Kaduna, HONORABUL FELIX HASSAN HYAT, ya kira taron manema labarai a Ofishinsa da ke shalkwatar Jam’iyyar a Kaduna. Inda ya bayyana masu gaskiyan abin da suka gay a wakana a zaben kananan hukumomin da aka yi a Jihar ta Kaduna, da kuma matakan dasuke da nufin dauka kan duk wuraren da su ka ga cewa ba a yi masu adalci ba. wakilinmu UMAR A HUNKUYI, ya halarci taron ga kuma abin da ya samo mana:

Yallabai yanzun kimanin mako guda kenan da kammala zaben kananan hukumomi a nan Jihar Kaduna, ba mu san abin da Jam’iyyar ku ta PDP ta fuskanta kan wannan zaben ba?

Tabbas an fuskanci matsaloli daban-daban a wannan zaben, wadanda kuma duk an kirkiro su ne. Da farko dai, ya tabbata hukumar zabe ta Jihar Kaduna mai zaman kanta kamar yadda ake fada, to lallai ashe ba mai zaman kan nata ne ba, inda a sarari sai ga shi ta hada kai da gwamnati inda aka yi ta yin abubuwan da ba mai tsammanin a yi irin su a wannan zamanin.

Da farko dai, muna da rahotannin duk abin da ya faru a kananan hukumomi daban-daban. Misali a nan, kananan hukumomin Giwa da Birnin Gwari, a Funtuwa ta Jihar Katsina ne aka tsinto kayan zaben na su. A kuma karamar hukumar Igabi, can a wata gona da ke Jaji, na wani hamshakin Jam’iyyar ta APC ne aka tara akwatunan zaben. A karamar hukumar Kajuru kuwa, Mai ba gwamnan Jiha shawara kan harkokin siyasa ne, Alhaji Uba Sani, ya je tare da Sojoji ya yi kane-kane a ranar zaben, bayan kuma ya bar wajen ne ya kira taro da jami’an da za su sanar da sakamakon  zaben, bayan zaman da ya yi da su ne, sai ga shi an neme su an rasa, sun bata-bat, har aka gama zaben ba tare da an ma san ina za a kai ba, don ba jami’an da ya kamata a baiwa, to a kusan ko’ina duk shigen rahotannin da muka samu kenan.

Sannan kuma sai muka gano cewa an canza ma su jami’an da za su bayar da sakamakon zaben a dukkanin kananan hukumomin ana gobe za a yi zaben. Sannan su wadanda ma aka canzan, mutanan mu ba su ma gansu ba, sai sanarwa kawai muka yi ta ji a kafafen yada labarai cewa, APC ta ci wannan karamar hukuma ta kuma ci waccan karamar hukumar.

Bayan hakan kuma, an bi cikin dare tare da Sojoji ana ta amfani da barkonon tsohuwa  ana tozarta mutane ana kwashe takardun zaben, an yi hakan a Kujama, an yi a Barnawa, an yi a Makera an kuma yi hakan a Kakuri Hausa.

Wuraren kuma ma da su da kansu sun rigaya sun shelanta wa duniya cewa mu ne a PDP muka ci zaben kamar a kananan hukumomin Sanga, Kagarko da Kajuru, sai ga shi don rashin kunya da rana tsaka wai hukumar zabe ta soke zaben Kajuru, ta kuma kwace na Kagarko ta kuma kwace Sanga ta baiwa gwamnati.

To irin wadannan abubuwan da suka yi ta yi ne ya sa muka ce lallai wadannan mutanan ba Dimokuradiyya ne nufin su ba, su na dai nu na karfin Soja ne kamar yadda muka gansu su na yawo da Sojojin gami da karfin ‘Yan Sanda da kuma iko da mulkin gwamnati, duk wadannan mun gansu kowa ma ya gansu kuru-kuru duk an yi amfani da su.

Amma abin da muka tabbata kan yadda muka ga al’ummar Jihar Kaduna bakidayansu daga dukkanin sassan Jihar sun ba mu goyon baya shi ne, in har zaben gaskiya kuma sakamakon gaskiya za a fadi, to ba yadda za a yi a ce Jam’iyyar APC ta sami sama da Kananan hukumomi uku a nan Jihar Kaduna.

To Shugaba, Jam’iyya mai mulki ta APC tana ikirarin cewa, ba a taba yin sahihin zabe kuma mai tsafta kamar wannan ba a nan Jihar Kaduna, ku a naku ba ku gamsu da yadda aka yi zaben ne ba?

Ina kuwa tsafta, tare da an saci akwatunan zabe an kai su har wata Jihar daban, an gama dangwale su an dawo da su, wannan shi ne tsaftan? An bi mutane da Sojoji da ‘Yan Sanda ana dukan su ana kwace takardun zabe, wannan shi ne tsaftan? Tsafta kenan ana gobe za a yi zabe a canza jami’an da aka tsara za su bayar da sakamakon zaben? Duk wannan abin da suke fada, kokari ne kawai suke yi na nannade tabarmar kunya da hauka, domin su a wajen su, abin kunya ne a ce, ga PDP ta tsaya zabe da su har ma ta cinye kananan hukumomin duka.

Kamar a wadanne Kananan Hukumomi ne kuke ganin PDP ta ci an danne mata?

Ka ga dai, Mun ci Kagarko sun danne, mun ci Sanga sun danne, mun ci Jaba, mun ci Kaura, sai suka ce wai sun soke za a sake yin wani zaben. Mun ci Kajuru sun soke, mun ci Kaduna ta arewa sun danne, Igabi kuwa ba a ma kai kayan zaben ba ballantana a san ko wane ne ya ci zaben, mun ci Sabon Gari sun danne, Birnin Gwari da Giwa kuwa, na shaida maka yanda aka kwashi kayan zaben aka kai Funtuwa, can wata Jihar ta daban. Mun ci Lere sun danne, mun ci Kubau sun danne, a Ikara kuwa, wajajen su Anchau ne aka kai kayan zaben gidan wani dan APC suka gama dangwale su, suka fito su na cewa wai sun ci zabe. mun ci Makarfi sun danne.

Hukumar zabe mai zaman kanta a nan Jihar Kaduna ta kira taron manema labarai jiya, inda ta sanar da sakamakon zaben duka. Ku kuna jin ba ku gamsu da wannan sanarwar na ta ba ne, akwai kuma wani mataki ne da za ku dauka a nan gaba?

Ko kusa sam ba mu gamsu da abin da suke fada ba, za kuma mu dauki wasu matakai. Tare da hakan, mu na rokon magoya bayanmu da su kwantar da hankalin su, don mu a kullum masu son zaman lafiya ne, ba kuma za mu yarda a yi amfani da wannan zaben ba wajen tayar da rikici a nan Jihar Kaduna ba. Amma za mu bi hanyoyin da doka ta tsara domin neman hakkin mu, za kuma mu je Kotu mu nemi hakkin mu. An yi zabe a kananan hukumomin Jaba da Kauru, suka ce sun soke saboda an yi rigima, alhalin mu har ya zuwa yanzun ba mu da wani rahoton wata rigima da aka yi a wannan zaben, da har zai kai ga cewa an soke zabe. akwatuna 110 ne a Jaba misali, sai suka ce wai an sami matsala a akwati guda, to da hakan sai a zo a ce an soke zaben duka?

Da ire-iren wadannan ne muka ga cewa muna da hujjoji masu yawa da za mu fito mu shaidawa duniya, za kuma mu hadu da su a Kotu, a can ne za mu ji irin rashin kunyan da za su gaya wa duniya. Amma a dunkule, rashin adalcin da aka tafka a wannan zaben, ya wuce misali.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: