Ibrahim Muhammad">

Zaben Kananan Hukumomin Kano, Abin Kunya Aka Jawo Wa APC – Sharada

Dan majalisar tarayya mai wakiltar Birnin Kano Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada ya bayyana zaben kananan hukumomi da ake cewa an.gudanar a jahar Kano kwanakin baya da cewa wulakanta jam’iyyarsu ta APC ne daga jagororinta na jahar Kano.
dan majalisar ya bayyana hakane a zantawarsa da wata kafar watsa labarai a Kano yayi nuni da cewa zaben tamkar wani wasan kwaikwayone da Gwamnatin Kano tayi amfani da tsabar kudi Naira Biliyan Biyu domin shirya shi.
Sha’aban Sharada Wanda tun bayan zaben fidda gwanin cikin gidan jam’iyyarsu na APC na fidda gwanin yan talarar shugabancin kananan hukumomi da kansiloli ya kalubalanci yanda aka gudanarda zaben yace basa tareda yanda akayi zaben na kananan hukumom.i Dama shugaban jam’iyyar na Jahar Kano ya fito karara ya bayyanawa Duniya cewa rubutawa zasuyi.
dan majalisar na tarayya mai wakiltar Birnin Kano yace wannan nema ya sa jam’iyyar hamayya ta PDP a kano.ta kaurace wa shiga zaben da akace anyi.
Yace bangaren magoya bayansu da suka nemi. shiga zaben fidda gwani a karamar hukumar Birnin Kano an hanasu duk wata dama da karfin tsiya, wanda da an tsaya an gudanarda zaben cikin gida bisa adalci da ra’ayin jama’a sunada yakinin samun nasara.
Sha’aban yace amma a karamar hukumar Birnin Kano an dauko mafi karancin goyon bayan al’umma da yanlele an kakabasu ance sune yan takara da akace sunci zaben,wannan abin.kunyane da tozarta jam’iyyar APC.

Exit mobile version