Madugun ‘yan adawar kasar kenya Raila Odinga, a yau laraba ya bayyana za su garzaya kotu domin kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da ya gabata a ranar 8 ga watan Agusta, ya yi watsi da kiran masu sanya ido na ya karbe sakamakon zaben da ya bayyan Uhuru Kenyatta a matsayin wanda ya lashe zaben.
Kimanin mutum 24 ne suka rasa rayukansu a hatsaniyar da ta biyo bayan zaben, ana ganin matakin da Odingan zai dauka kan iya haifar da cigaba da tarzoma a kasar.
‘Mun yanke shawarar garzaya wa kotun koli ne. Wannan shi ne matakin farko ba zamu amince da sakamakon ba’inji Odinga.
Odinga ya bayyana wa manema labarai a ranar juma’a da ta gabata ne hukumar zaben kasar ta ayyana shugaba Kenyatta a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’a miliyan 1.4, hakan zai bashi damar zarcewa a karo na biyu.