Sanata Mohammed Abba-Aji da Bukar Shuwa a karkashin jam’iyyar PDP, da ya yi takara a mazabar Borno ta tsakiya, Alhaji Mohammed Abba-Aji tare da Bukar Shuwa, a mazabar wakilai ta Jere, sun garzaya kotun sauraron karrakin zabuka, a birnin Maiduguri, wajen kalubalantar sakamakon da INEC ta nuna Kashim Shettima da Ahmed Satomi a matsayin wadanda suka lashe zabukan a Borno
Joe Kyari Gadzama ( SAN ), shi ne lauyan Abba-Aji, inda ya bayyana cewa wanda yake wakiltar ya kalubalanci sakamakon zaben ne bisa zargin murdiya tare da babakeren da ya gano a lokacin gudanar da zaben, wadanda suka ci karo da dokokin zabe- irin su cin zarafi, sayen kuri’un zabe, kana da kin amfani da na’urar tantance masu jefa kuri’a; wadanda su ka yi karan-tsaye da dokar zabe ta kasa.
Inda lauyan ya bukaci kotun sauraron koke-koken zaben da ta soke zaben tare da bayar da umurnin gudanar da wani ko ayyana wanda yake karewar a matsayin wanda ya samu nasarar zaben kujerar.
A tattaunawar sa da manema labarai, ranar jumu’a, a birnin Maiduguri, Sanata Abba-Aji ya bayyana dalilin da ya sa ya garzaya zuwa kotun saboda neman hakkin sa, biyo bayan gudanar da zaben mai cike da rashin tsari, a jihar Borno.
“Zaben cike yake da karen tsaye a dokokin zabe da rashin bin ka’idoji, kuma zaben cike yake da rudani, wanda idan doka za ta yi aikin ta; dole a soke shi, baki daya”.
“Ba a bayyana sakamakon a rumfunan zaben ba, kamar yadda yake a doka, inda maimakon haka sai aka dauke shi zuwa gundumomi da kananan hukumomi; wannan karya dokar zabe ne. Kuma muna da shaidun da zamu gabatar wa kotun a hannu, wanda yanzu haka mun bayar da wasu ga lauyan mu Joe Kyari Gadzama ( SAN )”.
A yayin da shi kuma Bukar Shuwa, dan takarar majalisar wakilai a karkashin jam’iyyar PDP, a mazabar Jere a zaben da ya gabata, ya bayyana daukar matakin garzaya wa kotun sauraron kararrakin zaben ne domin neman adalcin zargin haramben da aka yi masa, a matsayin sa na dan Nijeriya- domin karbar damar sa da aka kwace masa.
Bayanan koken da ya gabatar a gaban kotun, Shuwa wanda yake kalubalantar yadda hukumar INEC bisa ayyana Ahmed Satomi na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya samu nasarar lashe zaben kujerar majalisar wakilai, a wannan mazaba da ke kwaryar Borno a zaben 23 ga watan Fabarairun 2019.
“Saboda yadda mu ne jama’ar ta damka wa wannan damar, wanda kuma ina mai farin ciki da hakan, bisa yarda da suka yi damu, inda suka fito kwan su da kwarkwata a ranar 23 ga watan Fabarairu suka zabe mu a zuciya daya- amma aka murgude zaben ta hanyar aringizo da babakere, lamarin da ya saba da dokar zabe. Saboda haka zan yi amfani da doka wajen bin hakkin jama’a ta, wanda shi ne dalilin zuwa kotun sauraron karar zabe, domin neman adalci”. Ta bakin Shuwa.
A hannu guda kuma, a nashi bangaren, sakataren tsare-tsaren jam’iyyar PDP a jihar Borno, Kwamared Umar Bello, ya bayyana cewa za su mara wa yan takarar baya, wajen kwato hakkin su da aka kwace, ta hanyar zuwa kotun sauraron korafin zabukan.
Bello ya sake nanata cewa, jam’iyyar PDP a jihar Borno ta yanke shawarar garzaya wa zuwa kotun ne bisa dalilan take-taken da hukumar INEC ke nuna musu, jami’an tsaro tare da wasu yan siyasa daga wasu jam’iyyu, wadanda suka nuna wasu halaye sabanin doka da tsarin zabe.