Connect with us

LABARAI

Zaben Nijeriya: Babu Dan Takarar Da Za Mu Marawa Baya -Amurka

Published

on

Gwamnatin kasar Amurka ta ce ba za ta mara wa kowa ba a babban zaben 2019 na wannan kasar tamu, ta ce, bukatan ta, a zabi duk wanda ya yi nasara a zabe na gaskiya ba tare da murdiya ba.

“Za kuma mu yi duk mai yiwuwa domin taimaka wa gwamnatin ta Nijeriya,” in ji jakadan hulda da jama’a na ofishin jakadancin kasan ta Amurka da ke nan Nijeriya, Aruba Amirthanayagam, a lokacin da yake fadan hakan a Minna, ta Jihar Neja jiya, sa’ilin da ya kaiwa daraktan gidan Rediyon Prestige FM, Zabair Idris, ziyara.

Ya kuma bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da ta maimaita irin abin da ta yi a babban zaben shekarar 2015.Da aka tambaye shi ya yi bayani kan yadda Shugaba Donald Trump ya kwatanta Shugaba Buhari da mai “Wanda yake kama da babu,” a lokacin da Shugaba Buhari din ya ziyarce fadar ta ‘White House,’ sai jakadan ya ce, ba mu da bayanin makamncin hakan, wata jarida ce ta zo da shi, ita ya kamata ta yi bayani a kan shi.

Jakadan ya ce, “tabbas akwai wadanda suka fi karfin doka a Nijeriya, hakan kuma barazana ne ga tsarin dimokuradiyya.”

Ya yaba wa shugabannin gidan Rediyon kan yadda suke nu na kwarewa wajen tafiyar da aikin na su.

Ya kuma ce, gwamnatin Amurka za ta taimaka wa gidan Rediyon ta hanyar bai wa ma’aikatansa horo.

Babban daraktan gidan Rediyon, Idris, ya yi alkawarin za su ci gaba da yin aiki ba sani- ba sabo, ya ce su aikin yada labarai ne kadai suka sanya a gabansu.

 

 

 

Advertisement

labarai