Bello Hamza" />

Zaben Nijeriya: Za Mu Yi Maganin Masu Yunkurin Kawo Rikici -Sojoji

Shugaban Rundunar Sojojin Nijeriya, Tukur Buratai, ya bayyana cewa, rundunar ta shirya tsaf don bin umurnin da aka ba su sauda kafa, ya kuma yi watsi da kiran da Atiku Abubakar ya yi musu da kada su bi umurnin Shugaba Muhammadu Buhari na ba sani-ba sabo a kan masu shirin sace akwatin kuri’a a zaben da za a gudanar.
A ranar Litinin ne Shugaba Buhari ya umurci jami’an tsaro da su dauki tsatsaurar mataki a kan duk wanda yake kokarin sace akwatin dabe a zaben da ake shirin gudanarwa ranar Asabar.
A martaninsa, Atiku, dan takarar shugabancin Nijeriya a karkashin jam’iyyar PDP a zaben, ya ce, umurnin bai yi dai dai da tanade tanaden tsarin mulki ba, a saboda haka bai kamata kwamandoji su yi aiki da umurnin ba, ko da kuwa wa ya bayar da umurnin.
Amma da yake jawabi ga kwamandojin sojoji da manyan jami’an sojoji a jiya Laraba, Buratai ya nuna mamakinsa a kan yadda wasu dake neman mulkin kasar nan za su ingiza rundunar sojoji zuwa tashin hankali.
Duk da cewa, bai ambaci sunan Atiku, amma a bayyana yake cewa, yana tsokaci ne a kan dan takarar shugabancin kasar na na jam’iyyar PDP.
Da yake kara jadda sanarwa Buhari, Buratai y ace, duk wanda ya nemi katsakanda a harkokin zaben da za a gudanar zai dandana kudarsa kamar yadda ya kamata.
“Daya daga cikin aikinmu shi ne cikakken da’a ga shugabanni, amma abin takaicin shi ne yadda wani dake neman shugabancin kasar nan ke naman tunzura rundunar sojojji zuwa tashin hankali da kuma kin biyayya,” inji shi.
“Mun dade muna bayyana matsayinmu a harkokin siyasa, wanda shi ne na zama ‘yan ba tuwanmu a cikin harkokin siyasa. Amma tunzura sojojin Nijeiya na su yi tawaye ga shugabanni a karkashin mulkin dimokradiyya ba abin da za a amince da shi bane.
“Ina mai bukatar wannnan mutumin da ya janye wadannna kalaman neman tayar da hankalin da ya kawo mana. Ina kuma bayyana cewa, sojojin Nijeriya kwararru ne da suka tsayu a kan aikinsu, kuma tsayuwa da kwarewa a kan aiki yana dogara ne a kan da’a da biyayya ga shugabanin, in har kuma babu wannnan to lallai babu tsayayyan rundunar soja. Dole ne a samu sallamawa da da’a kashi bisa dari, a saboda haka ina mai tabbatar muku da cewa, za mu tsayu a kan wannan hadafin ga Nijeriya da ‘yan Nijeriya gaba daya.
“In har a kwai wani Dakare ko Haffasan soja da yake da kokwanto a kan yadda lamurra suke a halin yanzu, to yana da daga yanzu zuwa ranar 22 watan Fabrairu 2019 na ya yi murabu, don kuma ba za mu amince da rashin da’a ba a rundunar sojan Nijeriya a wannnan lokacin.”
Shugaban sojojin ya kuma kara da cewa, kwamandoji za su yi aiki da dukkan masu ruwa da tsaki a kungiyoyi don maganin duk wanda yake neman kawo cikas ga tsarin mulkin dimokradiyyar da ake ciki.
Ya kuma sanar da kafa rundunar ‘operation Safe Conduct’ wanda aka dorawa alhakin tabatar da an gudanar da zaben ranar 23 ga watan Fabrairu a na ranar 9 ga watan Maris a cikin kwanciyar hankali ba tare da wani matsala ba.
Tun da farko, jami’in watsa labaran rundunar sojojin, Sagir Musa, ya bayyuana wa ‘yan jarida cewa, sojojin za su yi aiki ne kamar yadda dokokin aikinsu ya tanada a lokacin zaben.

Exit mobile version