Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Zaben Osun: Waye Zai Dale Karar Gwamna?

by
4 years ago
in LABARAI, MANYAN LABARAI
3 min read
Har Yanzun Akwai Katin Jefa Kuri’a Milyan 7.9 Da Ba A Karba Ba –INEC
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

A jiya Asabar ne aka gudanar da zaben gwamnan da zai jagoranci jihar Osun da zarar ya samu nasarar kada sauran abokan takararsa, kawo lokacin da muke hada labarin nan a daren jiya INEC ba ta sanar da sakamakon zabe ba. a cikin ‘yan takarar duk wanda ya samu zarafi zai jagoranci jihar na tsawon shekaru hudu.

‘Yan takara kusan 48 ne suka nuna sha’awarsu na kasance a kujerar gwamnan a karkashin jam’iyyu daban-daban.

Daga cikin ‘yan takarar da suka fito neman sa’ar, biyar daga cikinsu ne ake kyautata zaton a cikinsu za a samu daya da mai nasara.

Labarai Masu Nasaba

‘Yan Bindigar Da Suka Sace Daliban Kwaleji 4 A Kaduna Sun Bukaci Kudin Fansa

Gwamnatin Ganduje Ta Kaddamar Da Aikin Gina Gidaje 500 A Kano

Iyiola Omisore, wanda tsogon mataimakin gwamnan jihar ne, ya fito neman kujerar a karkashin jam’iyyar (SDP); Gboyega Oyetola, tsohon shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, wanda ke neman sa’arsa a karkashin jam’iyyar (APC); Ademola Adeleke, Sanata ne wanda ke neman kujerar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar (PDP); har-wa-yau, tsogon sakataren gwamnatin Osun Fatai Akinbade shi ma na neman kujerar a karkashin jam’iyyar (ADC), shi ma wani tsohon sakataren gwamnatin jihar Moshood Adeoti ya fito neman gwamnan a karkashin jam’iyyar (ADP).

Sama da mutane miliyan daya ne suke da zarafin kada wannan kuri’un, kamar yadda hukumar zabe ta kasa ta shaida, sama da mutane 1,246,915 sun amshi katinsu na kada kuri’a daga cikin adadin 1,682,495 da suka yi rijistan kada kuri’a.

Wakilinmu ya labarto cewar rumfunan kada kuri’u sama da dubu 3,010 ne da suke fadin kananan hukumomi 30 aka samu gudanar da zaben a cikinsu.

Sai dai, an samu bayanai na cinikin kuri’u inda lamarin ya yi kamari, a yayin da wasu ke saye wa jam’iyyarsu kuri’u daga hanun masu kada kuri’a.

Tun kafin fara zaben na jiya dai, hukumar zabe INEC ta yi alkawarin gudanar da gaskiya da adalci a yayin gudanar da zaben, inda ta bayyana cewar da hadin guiwar jam’ain tsaro da wadanda abun ya shafa za su tabbatar da yi wa kowa adalci a yayin zaben.

An jibge masu sanya ido da masu nazarin zaben, inda bayan tattaro sakamakon zabe daga rumfunan zaben INEC za ta sanar da sakamakon zaben a sakatariyarta da ke Osogbo babban birnin jihar Osun, inda a nan ne za ta shelanta sabon gwamnan da ya samu nasara.

Da yake bayani wa ‘yan jarida, Gwamnan jihar ta Osun a halin yanzu, Rauf Aregbesola ya shaida cewar shi ba ya tunanin APC za ta samu matsala a zaben gwamnan Osun da aka yi jiya Asabar.

Rauf ya ce shi bai yi tunanin rashin nasara wa jam’iyyarsa ba don, a cewarsa, mutanen jihar suna son jam’iyyarsa.

A gefe guda kuma, a sakamakon korafin sayan kuri’u wanda ya yi yawa, kungiyar tarayyar Turai ta yi tir da saye da sayarwan kuri’u a zaben jihar Osun.

Wani jami’in masu sa ido a zabe na tarayyar Turai ya ce saya da sayarwan kuri’u ba abu mai kyau ba ne. A lokacin da yake zantawa da manema labarai, jami’in ya ce alamu sun nuna cewar hukumar zaben Nijeriya, INEC, ta samu ci gaba game da yadda take gudanar da zabe a zaben gwamnan a jihar Osun din.

A gefen rundunar tsaro masu tabbatar da zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali da tabbatar da an yi gaskiya da adacli wa kowani dan takara, rundunar ‘yan sanda ta sanya ido wajen dakile cinikin kuri’u da yakar masu kokarin kawo cikas.

Akalla mutane uku ne rundunar ta kama, kamar yadda suka wallafa a shafinsu na Twitter, wakilinmu ya shaida mana cewar a Karin farko ‘yan sandan sun cafke mutane biyu kan harkarlar sayen kuri’un zabe, inda daga bisani suka sake shaida sun kuma sake cafke wani karin mutum guda.

A daidai lokacin da ake tsumayar sakamakon zabe, ita kuwa INEC gargadi take kan wallafa sakamakon bogi.

Hukumar zaben Nijeriya (INEC) ta yi gargadi ga ‘yan Nijeriya game da wallafa jabun sakamakon zabe.

Hukumar ta fabi haka ne a wata sanarwar da ta wallafa a shafinta na Twitter inda ta ce duk wanda aka samu da wannan laifin zai fuskanci kotu.

Ta kara da cewa ita za ta sanar da sakamakon a hukumance.

 

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

NIS Ta Bayyana Adadin ‘Yan Kasar Waje A Nijeriya

Next Post

Ziyarar LEADERSHIP A YAU LAHADI Gidan Wazirin Kano: Dalilin Da Ya Sa Sarkin Kano Ke Kwato Hakkin Mata – Wazirin Kano

Labarai Masu Nasaba

2023: Kwamishinonin Ganduje 7 Da Ya Amince Da Ajiye Aikinsu Da Ukun Da Ya Yi Watsi Da Su

‘Yan Bindigar Da Suka Sace Daliban Kwaleji 4 A Kaduna Sun Bukaci Kudin Fansa

by Abubakar Abba
14 mins ago
0

...

Gwamnatin Ganduje Ta Kaddamar Da Aikin Gina Gidaje 500 A Kano

Gwamnatin Ganduje Ta Kaddamar Da Aikin Gina Gidaje 500 A Kano

by Abdullahi Muh'd Sheka
54 mins ago
0

...

‘Yan Arewa Masu Kai Abinci Yankin Inyamurai Su Dakatar Saboda Kisa –Matasan Arewa A Kudu

‘Yan Arewa Masu Kai Abinci Yankin Inyamurai Su Dakatar Saboda Kisa –Matasan Arewa A Kudu

by
7 hours ago
0

...

Babban Taron LEADERSHIP: Amfani Da ‘Mashahuran Hikimomi’ Zai Warware Matsalolin Nijeriya, In JI Manyan Baki

Babban Taron LEADERSHIP: Amfani Da ‘Mashahuran Hikimomi’ Zai Warware Matsalolin Nijeriya, In JI Manyan Baki

by Bello Hamza
8 hours ago
0

...

Next Post
Ziyarar LEADERSHIP A YAU LAHADI Gidan Wazirin Kano: Dalilin Da Ya Sa Sarkin Kano Ke Kwato Hakkin Mata – Wazirin Kano

Ziyarar LEADERSHIP A YAU LAHADI Gidan Wazirin Kano: Dalilin Da Ya Sa Sarkin Kano Ke Kwato Hakkin Mata – Wazirin Kano

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: