Umar A Hunkuyi" />

Zaben Ribas: Aikinmu Shi Ne Tabbatar Da Zaman Lafiya –Sojoji

A ranar Litinin ne rundunar Sojin kasar nan ta yi ikirarin cewa, “Aikinmu kadai a sha’anin zaben kasar nan, a Jihar Ribas da ma kasa bakidaya shi ne mu taimakawa hukumomi da ‘yan sanda wajen ganin an yi zaben cikin lumana.
Mukaddashin daraktan hulda da fararen hula na rundunar, Kanar Sagir Musa, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake mayar da martani a bisa zargin da aka yi wa rundunar na tsalma baki a sha’anin zaben Jihar Ribas.
Kakakin rundunar ya ce, Sojojin sun sami nasarar magance ayyukan wasu ‘yan banga mabiya son ransu, wadanda wasu ‘yan siyasa suka rena suka kuma ba su makamai da kayan Sojoji domin su ci zarafin abokan hamayyar su.”
Ya ce, “Mun ji zargin da ake wa Sojoji da ya shafi tsalma bakinsu a zaben Jihar Ribas. Wannan zargin ba gaskiya ne ba, musamman kasantuwar babu wata tabbatacciyar hujja ta tsalma bakin jami’an namu a baya can, a lokacin da kuma ma bayan zaben na 2019.
“Rundunar Sojin tana kara bayyanawa karara cewa aikinta a kan sha’anin zaben shi ne, taimakawa hukumomi da ‘yan sanda wajen ganin an gudanar da zaben lami lafiya.
“Duk wani zargi da ake yi wa Sojojin kamata ya yi a tabbatar da shi daga inda ya dace kafin a kai ga yanke hukunci a kai. A yanzun haka, babban hafsan Sojin kasa na kasar nan, Laftana Janar Tukur Buratai, ya kafa kwamitoci da za su binciki koke-koken da suka shafi yanda Sojojin suka gudanar da ayyukan na su a lokacin zaben.

Exit mobile version