Sulaiman Bala Idris" />

Zaben Shugaban Kasa: Hukuncin Kotu Zai Tabbatar Da Zabin ‘Yan Nijeriya –PSC

Kwamitin tallafawa Shugaban Kasa PSC ya bayyana kwarin gwiwa ga hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe zai yi a yau, wanda shi ne zai nuna zabin da ‘yan Nijeriya suka yi a babban zaben da ya gabata.
Kwamitin ya ce, a maimakon jam’iyyar PDP ta jira har zuwa kotu ta yi wannan hukuncin amma sai ta koma yin wasu irin abubuwa don kotu ta yi hukuncin da zai dadada musu. Wannan jawabi na kumshe ne a cikin takardar manema labarai da daraktan sadarwa da tsaretsare na kwamitin PSC, Mallam Gidado Ibrahim ya fitar a jiya.
Ya bayyana cewa; “akwai wani bidiyo da ke yawo a kafafen sadarwa na Intanet, inda a ka nuna ministan yada labarai, Lai Mohammed wai yana rokon ‘yan Nijeriya da su yafewa Shugaban Kasa Buhari kan rashin satifiket din kammala sakandare, don dai kawai kotu ta yi musu daidai.”
Ibrahim ya kara da cewa, irin kwallafa rai da ‘yan adawa suka yi kan wannan kujera ta shugaban kasa ba za ta bulle musu ba, domin buge-buge kawai suke yi a jeji. “Sun dauka kotu za ta biye musu ne kawai wurin yin hukuncin son rai.
“Bidiyon Lai Mohammed da ake yawo da shi, ba komi ba ne face aikin ‘yan adawa wadanda ke son kawo rudani a kasa.
Sune suka yi wa bidiyon kwaskwarima suka harhada shi don dai su haifar da rudani musamman ga hukuncin kotu na yau.
“Bayan sun gaza tabuka komi a zaben shekarar 2019 da ya gabata, inda suka so su sayar da Nijeriya ga wanda ya fi zuba kudi, PDP a wannan lokacin ta tsunduma cikin wasu irin munanan ayyuka don dusashe hasken kotun sauraron kararrakin zabe.
“Amma dai muna murna domin hukuncin yau zai bayyana hakikanin zabin ‘yan Nijeriya wadanda suka fito kwansu da kwarwatarsu wurin zaben Shugaban Kasa Buhari a watan Fabrairun da ya gabata.
Muryar al’umma ita ce muryar Ubangiji, kuma muna da yakinin cewa, Allah zai yi ikonsa a hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe za ta yanke.
Duk kuwa da kokarin jam’iyyar adawa na haifar da cikas. Daga karshe, Mallam Gidado Ibrahim ya bayyana cewa; “PSC na kira ga ‘yan kasa da su kwantar da hankalinsu, domin muna da tabbatacin cewa Buhari ne zai yi nasara hatta a kotun, domin ya ci gaba da ayyukan raya kasa da gwamnatinsa ta dauko.” Inji shi.

Exit mobile version