Umar A Hunkuyi" />

Zaben Shugaban Majalisa: Sabon Wakili Ya Bukaci Buhari Ya Jagoranci APC

Wani sabon dan majalisan wakilai ta tarayya a karo na farko daga mazabar Lere, a karkashin inuwar Jam’iyyar APC, Injiniya Ahmed Manir, ya bukaci shugaba Buhari da ya jagoranci tare da bayar da shawara ga Jam’iyyar APC wajen zaben sabon shugaban Majalisar wakilai ta kasa.
Injiniya Manir, wanda ya yi takara a inuwar Jam’iyyar ta APC, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, kuma ta shelanta shi a matsayin wanda ya lashe zaben na mazabar ta Lere, daga Jihar Kaduna, ya shawarci Buharin da kar ya bar wasu masu son zuciya su yi kane-kane a majalisun na tarayya kamar yanda suka yi a shekarar 2015.
Manir ya yi wannan maganan ne sa’ilin da yake tattaunawa da manema labarai a Jos, ranar Alhamis, ya ce a bisa sakamakon da hukumar zabe ta fitar ya nuna Jam’iyyar ta APC ita ce ke da rinjaye a cikin Majalisun na tarayya duka biyun, wanda hakan ya baiwa Jam’iyyar daman gyara kuskuren da aka yi a 2015, wajen sanya ma’abota son rai a shugabancin majalisun.
Manir ya bayyana jin dadinsa da godiya ga Allah a bisa nasarar da ya samu, ya kuma yi godiya ga masu zabe na mazabar ta Lere, a bisa yanda suka amince da danka ma shi amanar su zuwa majalisar.
[an Majalisar ya baiwa al’ummar mazabar na shi cewa ba zai ba su kunya ba.
Injiniya Manir, ya lashe zaben ne da kuri’u 64,442, inda ya doke abokin hamayyarsa, Alhaji Muhammad Lawal Rabi’u, na Jam’iyyar PDP wanda ya sami kuri’u 29,706, a zaben da aka yi a ranar Asabar, na shiga Majalisar Wakilan Ta Tarayya.

Exit mobile version