Zaben Shugabannin Jam’iyyar APC Ya Bar Baya Da Kura A Bauchi

 Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Dambarwar siyasa na neman kunno kai a cikin jam’yyar APC bayan da kwamitin shirya zaben shugabanin APC a matakin jihar ya kammala aikinsa, inda wasu bangaren suka nuna rashin gamsuwarsu tare da gudanar da wani sabon zaben na daban.

Wakilinmu ya labarto cewa a halin yanzu bangarori biyu ne ke ikirarin zama shugabanin jam’iyyar a matakin jihar wato Alhaji Babayo Misau da kwamitin da APC ta turo daga Abuja ya bayyana shi a matsayin wanda ya ci, a yayin da kuma wasu bangaren APC suka ayyana zaban Sunusi Aliyu Kunde a matsayin wanda zai zama shugabansu.

Wannan matakin ya janyo kungiyoyi daban-daban daga cikin jam’iyyar daga jijiyar wuya, inda suka nuna rashin gamsuwarsu da yadda aka gudanar da zaben tare da yin zargin cewa, Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ya musu karfa-karfa wajen yi musu dauki-daura na wanda ba su so a shugabancin jam’iyyar, don haka ne suka bayyana cewa masu ruwa da tsaki sun ki amince da zabin Adamu Adamu don haka ne suka gudanar da nasu zaben.

A wani hira da suka gudanar da ‘yan jarida, daya daga cikin bangaren da suka ayyana Sunusi Aliyu Kunde a matsayin shugabansu, sun bayyana cewar shi ne sahihin shugaba.

Mai magana da yawun bangaren, Hon. Adamu S. Noma, ya bayyana cewar kashi 80 cikin dari na mambobin APC suna bayan zaben Kunde, kuma ya bayyana zaben nasa ne na gaskiya.

Sai dai kuma shugaban kwamitin da uwar jam’iyyar ta turo daga Abuja domin shirya zaben, Jibrin Samuel ya bayyana Alhaji Babayo Misau na danbaren ministan ilimin a matsayin wanda ya lashe shugabacin jam’iyyar tare da sauran wadanda suka lashe kujeru su 35.

Samuel ya bayyana cewar ta hanyar amfani da tsarin daidaito ne suka kai ga gano wadanda suka ci zaben, ya ce kwamitinsa ya tabbatar da abin da masu ruwa da tsaki a cikin jam’iyyar jihar ne suka yi.

Ya kuma bayyana cewar sun tafiyar da komai bisa tsarin da aka ba su daga shalkwatar jam’iyyar ba tare da kauce wa ka’ida ba, sai ya nuna cewar sun yi zaben bisa nagarta.

Exit mobile version