Idris Umar" />

Zafi Ya Kashe Yara 2 A Cikin Mota A Samarun Zariya

A ranar Juma’ar satin data gabata ne jama’ar anguwa Hayin Dogo Samaru layin na Moriki da ke karamar hukumar Sabon Gari ta tsinci kanta cikin jimami da firgici bisa yadda wasu yara suka kulle kansu a cikin wata mota da ba a sani ba har zafi yayi sanadiyyar mutuwarsu har lahira.
Wakilinmu ya ziyarci anguwar da lamarin ya faru.


Isma’il Lawal da Usaini Dahiru duk yara ne yan shekaru 5 kuma sun kasance abokai ne bisa yadda sukaga iyayensu suna tare da juna a matsayin makotaka a wannan anguwa da ake kira layin na Moriki Hayin Dogo Samaru.
A ranar juma’a kafin zuwa masallaci ne Isma’il da abokinsa Usaini suka sammaci idanun jama’a suka afka cikin motar makobcin su da ake fakin dinta a wani sako da jama’a basu cika bi ta wajan ba illa mai aje motar
Kasancewar yaran sunga ba kowa ke zuwa wajan motarba yasa sukayi amfani da wannan damar suka kutsa cikin motar ba tare da Kowa yaga lokacin da suka shigaba suka ci gaba da wasa.
Bayan gama wasanne kuma sai suka kasa fitowa daga cikin motar har tsawon awanni 5 zuwa 6 gashi motar kiran zamani ne babu inda iska ke shiga ko na kafar allura ga zafin rana da ake zabgawa irin ta juma’a.
Wannan yanayi da yaran suka shiga na rashin shakar iska ga zafin rana ne yayi sanadin rasuwar yaran guda biyu take a daidai lokacin da iyayen suke cikin gari don bayar da cigiya.
Anga gawarwakin Isma’il da Usaini ne lokacin da kanin mai motar yaje amfani da motar inda daga zuwa ya bude don yin amfani da motar kwatsam sai ga gawan yaran a kwance da alamun sun nemi agaji amma tunda motar tana nesa ne da hanyar da mutane ke bi hakan yasa basu sami taimako ba hakan yakai ga yaran duk sun rasa rayukansu baki daya.
Malam Dahiru shi ne Uba ga Usaini kuma shi ya yi magana a madadin iyayen yara da shi kansa wanda ya aje motar da yaran suka shiga suka rasa rayukansu.
Malam Dahiru ya tabbatar da rasuwar yaran guda 2 kuma yace, babu abin zasuce illa Allah ya gafatta masu kuma ya tabbatar da cewa basu da wani ja face mika kukansu ga Allah don kare sauran yaran nasu
Malam Dahiru ya kara da cewa, bisa yadda suke zaman amana a wannan anguwa don haka yace yana roko ga jama’a dasu kiyaye da inda zasu rika aje motarsu don gujewa kara faruwar irin haka kuma yayi fatan Allah ya gafattawa yaran nasu
Ya zuwa hada wannan rahoton DPO mai kula da shiyar ta Samasu ya bayar da damar yiwa yaran sutura tare da gaiyyatar dukkan bangaren da lamarin ya shafa don shigar da lamarin cikin kundinsu.

Exit mobile version