Connect with us

LABARAI

ZAGIS Ta Yunkro Wajen Tabbatarwa Masu Filaye Da Filayensu A Zamfara 

Published

on

Hukumar tattara bayane na taswurar jihar Zamfara watau (Zamfara Geographic Information System) ta yunkuro wajan tabbatar wa masu filaye da gidaje filayan su a fadin jihar Zamfara batare da sun salwanta ba .

Darakta Janar na Hukumar ZAGIS, Hon Hassan Idiris Gusau, ne ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa ga manaima labarai a ofishinsa da ke cikin hediwatar hukumar da ke Gusau ,babban birnin jihar Zamfara .

” Hon Hassan Gusau ya bayyana cewa , akwai wani take da akewa wannan hukuma na Filinka ko gidanka hakinka ne ya za’ayi ya zama hakinka shi ne , kazo ZAGIS kayi rijista a baka satifiket , wannan fili babu Wanda ya isa ya cimashi ko da gwamnatin ke bukatar shi zata amsheshi da daraja sakamakon kayimasa rijista . dole ta biyaka yadda ya kamata. kuma babu wani mai kudi ko kamfanin da ya is a ya cinma fili indai kana da wannan rijista , dan kai kadai keda ita inji Daraktan .

” Da ya koma kan wasu manyan ayyukan hukumar, Daraktan ya bayyana cewa , ‘ A kwai taskace tarihin jihar Zamfara ,da kuma tara kudi na dukan bayanan da ke cikin Ma’aikatun jihar, wanda duk wanda ke neman bayanai akan jihar Zamfara idan ya shigo ZAGIS zai samai shi da yardar Allah, inji Darakta Janar.

” Kuma wannan hukumar ba cima zaune bace ba , dan tana da mayan shiri na samarwa jihar Zamfara kudin shiga a lokacin da take tafiyar da ayyukan ta a fadin jihar da ma wajanta.

” Hon Hassan ya kuma tabbatr da cewa, ‘ mun samu cikaken goyan baya ga mai daraja gwamna Bello Matawallen Maradun akan tafiyar da wannan hukumar dan gani ayyukan ta na cigaban jihar bai samu na kasuba.

” A karahe Daraktan Janar Hon Hassan Idris Gusau , yayi kira ga alummar jihar Zamfara, da su gaggauta shigowa wannan hukumar dan karin samun bayane na ayyukan ta a koda yaushe.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: