Connect with us

RAHOTANNI

Zai Shafe Wata 8 A Gidan Yari Kan Satar Wayar Salula

Published

on

Wata Kotu dake zaune A Abuja a Karmo, mai Daraja Ta farko(1) Ta yanke wa Chukwu Nduku, mai shekara 37 zaman gidan yari na tsawon wata 8 saboda wata wayar salula da ya sata.
Mai sharia Mr. Inuwa Maiwada yabawa wanda ake zargi da satan daman fansar kanshi akan kudi naira N11,000 sannan kuma yaja kunnanshi da yazama mai kyakkyawan hali.
Maiwada kuma ya Umarce shi da yabiya wanda ya kawo karar kudi naira N60,000.
Wanda ake zargi da satan tuni ya yarda da laifin da yayi, kuma ya roki alkali da yayi sassauci da hukunci da rahama akanshi.
Ya gayawa kotun cewa, bai san meyazo kanshi ba har ya aikata wannan laifi.
Munji cewa dai, wanda ya gudanar da bincike akan wanda ake kara, Ijeoma Ukagha ya shaida wa kotun cewa, wanda ake zargi ya tabbatar da aikata wannan laifi ya kuma roki yafiya.
Tace, Laifin yayi Dai-dai da abinda doka ta tanada na cikin kundin sharia bangaren 79 da 288 na Penal Court.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: