Zai Yi Wahala Na Sake Bugawa Faransa Wasa -BENZEMA

Ɗan wasan gaba na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid, Karim Benzema ɗan ƙasar faransa ya bayyana cewa baya tunanin zai sake bugawa ƙasar ta ta faransa wasa inda mai koyar da yan wasan ƙasar na yanzu, Didier Deschamp shine zai cigaba da jan ragamar ƙasar.

Kusan shekaru biyu kenan ɗan wasan bai bugawa faransa was aba sakamakon zarginsa da akeyi na fitar da wani fefen bidiyo wanda ɗan wasan ƙasar faransa, Balbuena yake saduwa da wata yarinya.

Rahotanni sun bayyana cewa Benzema da wasu mutane sun fitar da bidiyon ne domin su batawa ɗan wasan suna wanda daga baya aka gane kuma aka fara tuhumar su.

Benzema, mai shekaru 29 yace baya tunanin zai sake saka riga domin wakiltar ƙasar anan kusa sai dai yace yakamata mai koyar da yan wasan ƙasar ta faransa daya mayar da hankali wajen ganin ƙasar ta samu nasara ba wai abinda yafaru a bay aba.

Yaci gaba da cewa bashi da matsala da kowa acikin yan wasan ƙasar ko kuma masu horarwa, kawai dai hukunci ne akayi masa kuma ya haƙura ya karba yana kuma yiwa ƙasar fatan alheri.

A ƙarshe yace yana fatan ƙasar zata samu lashe kofin duniya na wannan shekarar saboda sunada yan wasan da zasu iya taimakawa ƙasar wajen cin kofin.

Ɗan wasan kuma dai yana fama da rashin zura ƙwallo a raga sakamakon har yanzu ƙwallo daya yaci a ƙungiyarsa ta Real Madrid  cikin wasanni 9 daya buga a ƙungiyar a wannan kakar.

Exit mobile version