Zaizayar Kasa Ta Yi Ajalin Mutum 20 A Kamaru

A Jamhuriya Kamaru mutane 20 ne aka rawaito cewa sun rasa rayukansu sakamakon wata zabtarewar kasa, da ta biyo bayan ambaliyar ruwa da aka samu a birnin Bafusam dake yammacin kasar.

Wasu bayanai da gidan Talabijin din kasar na CRTV ya fitar sun ce adadin mutanen da suka mutu a lamarin ya karu zuwa 20, haka kuma akwai yiyuwar adadin ma ya karu.

Tun da farko dai an ruwaito cewa mutum 11 ne suka rasa rayukansu sakamakon zabtarewar kasar, da ta yi rusa wasu gidaje.

Lamarin dai ya auku ne a cikin daren jiya Litini wayewar safiyar Talatar nan sakamakon ruwan saman tamakar da bakin kwarya da aka samu a cikin kwanakin biyun nan a yankin.

Bayanai daga kasar sun ce masu aikin cewa sun fiddo gawarwakin mutane 11, a daidai lokacin da kuma suke ci gaba da neman wasu mutane kimanin hamsin da suka bata.

Ko baya ga hakan da akwai gidaje da dama da motoci da suka lalace.

Exit mobile version