Zaman Dardar: An Sake Sanya Dokar Hana Fita A Jos

Gwamnatin Jihar Filato ta sake saka dokar hana fita kwatakwata a cikin garin Jos ta Arewa bayan harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a a kauyen Yelwan Zangam. Mai magana da yawun gwamnan jihar, Dr Makut Macham, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a yau Laraba.

Matakin na zuwa ne bayan far wa kauyen Yelwa Zangam da ke gundumar Zangam a Jos ta Arewa da wasu mahara suka yi, inda suka kashe kusan mutum 30, kodayake hukumomi ba su tabbatar da adadin mutanen ba.

A cewar Gwamna Simon Lalong, dokar hana fitar ta awa 24 za ta fara aiki ne daga 4:00 na yammacin Laraba 25 ga watan Agusta har zuwa sanarwa ta gaba.

Exit mobile version