Rabiat Sidi Bala" />

Zaman Gidan Ya Isa Haka Nan, In Ji Wasu Daliban Nijeriya

A ci gaba da tattaunawa da wannan shafi yake da dalibai game da hutun makarantu da ake na Korona, dalibai da dama sun koka da irin zaman gidan da suke yi wanda ba shi da ranar karewa kamar yadda wasu suke fada, a ganinsu wannan zaman ba komai ba ne face ci baya ga karatun nasu, wasun su, sun kara kokawa game da zaman gidan ba tare da karatu ba sakamakon rashin samun gurbin shiga makarantar gaba da sakandare da suka rasa wanda a cewar su ba don zaman da ake a gida ba da tuni suna nan suna karatunsu, kuma da karatun nasu ya yi nisa.
Ta wani bangaren kuma, daliban sun nuna jin dadinsu bisa zaman gidan da ake ba tare da sun je makaranta ba sakamakon karatun da suke ta online. Wasu daga cikin daliban kuma sun ba da shawarwari ga manyan da suke da damar janye wannan al’amari inda suka kawo shawara mafi sauki kan cewa ya kamata a saka doka ga duk dalibin da zai shiga makaranta dole ne ya zama ya kare kansa kamar yadda ake ta sanarwa don gujewa kamuwa da cutar, kamar saka takunkumi a fuska, da wanke hannaye da shafa sinadarin wanke hannu ba wai a zauna a gida shekarun karatun suna wucewa ba. Ga dai yadda ta kasance daga bakin wasu daliban:

Hajara Sidi Bala:

Hajara Sidi Bala

Hajara Sidi Bala wadda aka fi sani da Dakta Sidiyah, Daga makarantar KSP School of Technology Matan Fada Road. A gaskiya matakin da gwamnati ta dauka dangane da hutun Korona ya yi yawa saboda an samu nakasu da dama ta bangaran karatu, musamman ma wadanda suke matakin rubuta jarabawar nan ta SSCE, komai ya tsaya cak! abin damuwar ma a nan shi ne ba makaranta sannan kuma ba sana’a, haka shi zai janyo karayar tattalin arziki a wannan kasa tamu mai albarka. Shawara ta a nan ita ce ya kamata a duba koken ‘yan makaranta saboda rashin bude makarantu ba mafita ba ce kuma in an kulle boko meye laifin islamiyya? A gaskiya ya kamata a duba a bude mana makarantu. Na gode Allah ya sa a duba.

Jabeer M.Hassan (Jaheed):

Jabeer M Hassan

Wannan a matsalar makarantun Sakandare da firamare kenan, wadanda su ne suke da karancin matsala fiye da matasan da suke zaune a Jami’o’i da sauransu, saboda mafi yawansu akwai iyaye ko wani daga cikin dangi da yake daukar nauyin karatun. Matasa su ne kashin bayan al’umma, ko kuma na ce wani ginshiki mai karfi da yake rike da al’ummar wannan zamani, mafi yawan wadanda suke makarantun gaba da sakandare Matasa ne da ‘yan mata, a wannan lokaci karatun mafi yawan matasanmu na gab da lalacewa, musamman idan aka ci gaba da rufe makarantu. Idan har zai zamto za a iya bude kasuwanni da Masallatai, me zai hana a bude mana makarantu dalibai su koma?. Batun karatu Online ba (Karatu ta yanar gizo) kowane yake iya yi ba, don ba kowa ne yake daukar abin da gaske ba, kasancewar mu a nan Nijeriya karatun bai yi yawa ba, shi ya sa idan ka ce kana karatu online da yawa ba sa daukar ma karatun kake yi, balle a kai ga wahalar karatu, shin idan aka ce karatun online za a yi a wannan shekarar ya za a yi da wadanda karatun lafiya suke (Medical Doctors, Nurses, Lab Scientists, Microbiologists, computer Scientist, Pharmacists, Agriculturalists, Opthalmologists etc) duk wadannan karatun su yana tafiya ne bisa ga Jarabawar gwaji (Practical), ya ya za a yi da su, ko su ma online din za a nuna masu yanda ake yi? Ba wanda zai rika monitoring din su a dakin gwaji (Lab)
Kin ga kenan karatun su ya tsaya cak, don ba na tsammanin karatunsu zai iya tafiya online, ko yana iya yiwuwa online din sai kadan daga cikin su, kamar Computer scienctist da Sauransu, sauran kuma ya za a yi da su kenan? Karatun su ya lalace. Shawarata Ya kamata gwamnati ta duba al’amarin karatun mu matasa, domin da yawan mu an saba mana lamba, mun yarda da kaddara, domin zuwan Korona kaddara ce wacce ba a kauce mata, hakan ya janyo tabarbarewar ababe da yawa, daga ciki kuwa har da kasuwanci, ya kamata gwamnati ta duba yawan fyade, kisan kai da sace-sace da yake ta kara yaduwa a kasar nan, ina ga ba ta hanyar da zai ragu ko a dakile shi gabadaya face ta hanyar Ilmantar da matasa, akwai matasa da yawa da idan aka ce karatunsu sai wata shekara shikenan karatun ya lalace.
Idan akwai hali ya kamata gwamnati ta duba yiwuwar bude makarantu, don da yawan matasa sun koka, iyayen yara sai korafi suke akan rufe makarantu na ba gaira, ba dalili, wanda gwamnati take ci gaba da yi tun bayan bullowar cutar Korona. Muna rokon Allah ya dafa mana, ya shige mana gaba, ya kuma sanya wa karatun mu albarka, Allah ya kawo mana karshen kashe-kashe da ta’addanci a kasar nan.
Jabeer M Hassan (Jaheed) dalibi a Jami’ar Kimiyya da fasaha da ke Jihar Kebbi. (Kebbi State Unibersity of science and Tecnology).

Zainab Muhammad:

Zainab Muhammad

Sunana Zainab Muhammad, daga Jami’ar Bayero Unibersity, Kano. Na farko dai wannan cuta ta Korona ta kawo nakasu sosai a karatu domin ta mai da mana karatu baya sosai, sannan ta sa da yawa daga cikin dalibai yara har ma manya an manta wasu darsussun da malamai suka koyar kafin bullowar cutar ta Korona. Na biyu, shi ne akwai daliban da ya kamata a ce a wannan shekarar za su kammala karatunsu.
Kamar ni nan, wannan shekara ta 2020 ce ta kammala karatuna, wanda a yanzu ba mu san takamaimai lokacin komawa ba balle musa rai da gamawa. Hakan ba karamin ciwo ya yi min ba, sai dai fatan rabbi ya sa hakan ne alkhairi a gare mu bakidaya. Ba ma mu dalibai ba, wannan cuta ta durkushe kowa ta dawo da kasarmu baya kamar yadda da ma mu Nijeriya kodayaushe mu ne a karshe.
Ma’aikata da ‘yan kasuwa, wasu Malaman makaranta ne ta kudi ta jawo masu rashin biyan albashi, su kuma ‘yan kasuwa rashin bude kasuwanni a kullum kamar yadda aka saba, da kuma hanawar shigowa da sabbin kaya daga kasashen ketare. Na uku, game da yadda gwamnatinmu da ta lissafa wasu dokoki wanda za a bi in dai ana so a koma karatu yadda ake so na nesantawa tsakanin dalibi da dalibi wajen zama a aji, su taimaka a yi mana hakan don mu koma karatunmu. Ina kira ga dalibai da sauran mutane baki daya da zaman nan ba zai karar da mu da komai ba saboda haka mu tashi mu samu abin yi domin taimakon kanmu, kamar ni ina yi wa yara masu darasin Sakadare da Firamare domin taimakon su da kuma taimakon kaina yau da gobe, domin mu ba mu da wata hanya da za mu ce ga ta mun kawo ta magance cutanan sai daga manyan mu kuma Allah Subhanahu Wata’ala ne zai fidda mu ba dabarar mu ba. A nan zan tsaya bawai don na gama ba, sai don na ba wa wasu damar tofa albarkacin bakinsu. Na gode.

Exit mobile version