A cI gaba da kokarin da Majalisar mahaddata Alkur’ani ta kasa reshen Jihar Kano keyi na gudanar da saukokin Alkur’ani Mai girma 313 a kowacce karamar Hukuma, ranar lahadin data gabata Majalisar Mahaddata Alkur’ani na karamar Hukumar Gaya suka gudanar da wannan kyakkyawan aiki inda aka gudanar da Saukokin Alkur’ani 313 domin rokon Allah ya magance mana matsalar tsaro da annobar Korona da ke zaman barazana ga wannan Kasa tamu mai albarka.
Galadiman Gaya Alhaji Abubakar Abdulkadirya bayyana farin cikinsa bisa wannan aikin alhairi da alarammomi suka gudanar wanda yace itace hanya daya tilo da ka iya kawo karshen halin da al’umma musamman arewacin kasarnan ke Ciki, daganan sai bukaci Mahaddata Alkur’ani da a cI gaba da wadannan addu’o’i domin Dorewar Zaman Lafiya.
Shi ma da yake gabatar da jawabinsa shugaban Majalisar Mahaddata Alkur’ani na Kasa Gwani Aliyu Saluhu Turaki babban limamin Masallachin Juma’a na Alhassan Dantata dake Kano, ya bayyana gamsuwa kwarai da gaske bisa kyakkyawan tsarin da aka gudanar da wannan taron Addu’a.
Gwani Aliyu Saluhu Turaki yace wadannan addu’o’i ana gudanar dasu a matsayin gudunmawar mu domin samun afuwar Allah kan halin da ake ciki, kuma alhamdulillah wannan aiki muna yin ne a kashin kanmu, sai dan abinda wasu masu kishin Alkur’ani da kaunar zaman lafiya suke bada irin tasu gudunmawar. Daganan sai jadadda aniyar wannan Majalisa ta Mahaddata na ci gaba da gudanar da wadannan addu’o’i a daukacin kananan Hukumomin Jihar Kano 44.
Gwani Muhammad Auwalu Isah Gaya shi ne shugaban Majalisar Mahaddata Alkur’ani na Karamar Hukumar Gaya, kuma Shugaban Mahaddata Alkur’ani na yankin Masarautar Gaya, ya bayyana cewa hakkin ‘yan uwa ne gudanar da irin wadannan addu’o’i musamman a irin wannan likaci da ake tsananin bukatar addu’a, saboda haka sai ya Jinjinawa Alarammomi bisa amsa wannan gayyata, sannan ya isar da godiyar Mahaddata Alkur’ani ga Masarautar Gaya bisa kulawa da kishin zaman lafiyar al’ummar wannan Karamar Hukuma, Jiha da Kasa baki daya.
Haka Kuma adai wannan Rana aka gudanar da bikin saukar Karatun dalibai 6 da suka haddace Alkur’ani a makarantar Shugaban Malisar Mahaddata Alkur’ani na Karamar Hukumar Gaya, Wanda a lokacin saukar shugaban Majalisar Mahaddata Alkur’ani na Kasa Gwani Aliyu Saluhu Turaki ya nada Gwani Muhammad Auwalu Isah Gaya a matsayin Gangaran.
Alarammomi daga yankunan mazabun Karamar Hukumar Gaya ne suka halarci wannan taron Addu’a, sai kuma baki daga makwabtan wannan Karamar Hukuma da daruruwan mutane ne suka shaida wannan muhimmin taro.
Su Sanata Gaya Sun Halarci Sadakar Kwana 40 Na Surukarsa A Ankpa
Daga Ahmed Muh'd Danasabe, Lokoja Ranar Lahadi da ta gabata...