Yusuf Abdullahi Yakasai" />

Zaman Lafiya Ne Jagoran Ci Gaban Kowace Kasa – Galadiman Bauchi 

Galadiman Bauchi

Alhaji Abubakar Yalwa Mainan Galadiman Bauchi, ya ce, babu wata kasa a duniya da za ta ci gaba matukar babu zaman lafiya da kwnaciyar hankali ga al’ummarta. Yalwa, ya yi wannan jawabi ne a wani taron da ‘yan jaridu inda ya nuna farin cikinsa na shigowar sabuwa 2021.
Haka Zalika ya nuna bakin cikinsa da wasu abubuwa da suka faru a baya da kuma yanzu dangane da abin da ya shafi rashin tsaro, da suka hada da Boko Haram da sace-sacen mutane. A kan haka ya yi addu’ar fatan Allah ya kawo mana dauki.

Maina ya yi roki gwamnati idan za a dauki ma’akatan tsaro a duba da kyau a tantance kafin a dauka gudun kada a dauki masu laifi. Bugu da kari Mainan, ya roki jama’a su dinga ba da shawara ta gaskiya, domin hakan ita hanya daya da kasarmu za ta samu ci gaba.

Sannan ya roki jama’a da su kiyaye dokokin Korona domin kaucewa yaduwar cutar, ya kara da cewa dole sai jama’a sun ba wa jami’an tsaro hadin kai da goyan baya wajen bayar da sahihan bayanai domin dakile aikata laifuka. A karshe ya yaba wa Gwamnatin Tarayya da ta jihohi da jami’an tsaro kan irin namijin kokarin da suke a ayyukansu.

Exit mobile version