Ganin cewar zaman lafiya ne yafi komai dadi a rayuwar dan adam ta duniya a wajen gudanar da harkokinsa na yau da kullum bisa ga wannan dalilin ne ya sanya sarkin al’ummar arewacin Nijeriya mazauna unguwar Aja ta karamar hukumar Itiwosa dake cikin garin Legas, Alhaji Ibirahim Goma ya shawarci al’ummominsa guda biyu Hausawa da sauran kabilun arewacin Nijeriya mazauna unguwar Aja dasu cigaba da zaman lafiya da junansu dama sauran kabilu mazauna unguwar baki daya, Sarki Ibirahim Goma ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da yake karbar bakuncin wadansu matasa ‘yan kabilar Yarabawa da suka zomasa gaisuwar bangirma kuma ya tara mutanen sa da yake shugaban ta a wan nan unguwa ta Aja suka zauna suka gudanar da taro domin kara nemo hanyoyin cigaba da zaunawa lafiya a tsakanin su baki daya bayan sun kammala wan nan taron nasu ne ya sallami bakin sa suntafi gidajen su sai Sarki Ibirahim Goma ya cigaba da gudanar da wani taron nasu nagida tare da al’ummar sa ta arewacin Nijeriya mazauna unguwar Aja domin tat taunawa abisa wadansu matsalolin da suka shafi unguwar ta Aja domin warwaresu anan take inda ya fara da cewar farko dai ya wajibta akansu a wajen cigaba da hada kawunan junansu domin neman kariyar mutun cin junansu a wajen gudanar da harkokin su na yau da kullum a tsakanin su da sauran kabilu mazauna yankin ya kara da cewa san nan kuma wajibi ne su cigaba da fadada hanyoyin da za su cigaba da kawo masu zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin su da sauran kabilu mazauna yankin na unguwar ta Aja da Legas baki daya sannan Sarki Ibirahim Goma ya cigaba da shawartar mutanen nasa da yake jagoran ta a unguwar ta aja dasu guji aikata duk kan wani kokuma wani abu da zai kawo rar raba kawunan al umma a unguwar ta Aja da Legas dama Nijeriya baki daya ya kara da cewar kuma wajibi ne gasu mabiya dasu cigaba da bin ummurnin shuwagabanni su a kowanne lokaci a matsayin su na mabiya domin shuwagaban nin su cigaba da kare masu mabiyan nasu mutuncin su ta kowanne bangaren da fatan Allah ubangiji ya cigaba da zaunar da Nijeriya lafiya karshen ya cigaba da cewa yana isar da sakon sa na taaziya ga al’ummar Hausawa da sauran kabilu na arewacin Nijeriya mazauna cikin garin Legas bisa ga rasuwar wadan su daga cikin shuwagabannin su anan Legas ya ce na farko Aarki Mai Sale wanda shima ya taba zama wani abu a cikin shugaban cin barebarin jihar legas wan da Allah ya yi masa rasuwa ta sanadiyar gajeruwar rashin lafiya a kwanakin baya da fatan Allah ubangiji ya gafarta masa da rahama ya cigaba da cewa haka ma Aarkin al’ummar Hausawan Legas Alhaji Sani Kabiru wanda shi ma Allah ya yi masa wa’adi ta sanadiyar gajeruwar rashin lafiya, ya ce, shima yana yi masa fatan Allah ya gafarta masa, sai na ukun su na baya bayan nan Sarkin Barebarin jihar Legas Alhaji Mustafa Muhammed wanda shima Allah ya yi masa cikawa a farkon satin nan da ya gabata ya ce kuma duk kan su sun bada gummawar su ta musamman a wajen hada kawunan al’ummar arewacin Nijeriya mazauna cikin garin Legas da fatan Allah ubangiji ya jikan su kuma ya gafar ta masu da rahamar Amin.