Zaman Lafiya Shi Ne Mutuncin Rayuwar Da’ adam A Duniya

Tsohon ministan shari’a alokacin sardauna Jostis Mamman Nasir Galadiman katsina hakimin malumfashi, ya ce zaman lafiya shi ne mutuncin dan dan’adam a duniya a cewarsa sai da lafiya ne ake neman kudi ake cin abinci ake yin aiki zirga-zirga ta yauda kullum ake neman ilimi na Arabic dana boko da sauran makamantansu

Tsohon ministan ya yi wannan kalami ne a yayin da wata tawagar matasa  na garin Malumfashi suka zo masa gaisuwar bangirma da kuma godiya game da yanda yake ba al’umar Malumfashi shawarwarin da ke amfanarsu a cewar  uban kasar wajibin jamar jihar Katsina garin Malumfashi da Nijeria baki daya su zama masu bin dokar kasa da bin shuwagabanni da ba su  girman da Allah ya ba su da aikata kyawawam  ayyukan a aikace domin koya wa yara kanana da ke tasowa tarbiya mai kyau ya ci gabada da cewar suma da kuma nuna wa na kasa halaye nagari dominsasu hanyar gaskiya

Da ya juya kan maganar ilimi kuwa cewaya yi wajibi ne kuma su san ya masu ido da jajircewa har sai sun ga yaran sun samu ilimin  nan guda biyu Arabic da kuma  boko sanan ya ce annabima  ya ce ajene man ilimi harbirnin sun ya ci gaba da cewar tsantsu baya tashi da fuffuke daya sai dai guda biyu

Galadiman ya kara da cewar bai jidadi ba game da wadansu jihohin Nijeria da ke fama da rikice-rikicen siyasa da fashi da makami  na barayin shanu da sauran  makamantansu ya ce yakamata ‘yan Njjeriya su ci gaba da yin addu’o’i domin a samu saukin wannan lamari sannan ya nuna farinkinsa wajan ganin shugabansa janar Muhammadu Buhari ya dauki matakin kashe wadannan miyagun ayyuka.

 

Exit mobile version