Daga Yusuf Shu’aibu,
A ranar Alhamis ce, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, zaman lafiyar Jamhuriyar Nijar shi ne na Nijeriya kasancewarsu makota na kusa. Domin haka, ya bukaci shugaban kasa mai barin gado Mahamadou Issoufou da mukarraban gwamnatinsa su martaba kundin tsarin mulkin kasar wajen gudanar da zabe karo na biyu a ranar 21 ga watan Fabrairun shekarar 2021.
A cewar kalamun mashawarcinsa ta fannin yada labarai, Femi Adesina, shugaban kasan ya bayyana hakan ne lokacin da yake amsar bakuncin tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo wanda shi ne shugaban jagoran kungiyar ECOWAS a kan zaben kasar Jamhuriyar Nijar.
Shugaban kasa Buhari ya taya Sambo murna a matsayin wanda ya jagoranci zaben, inda ba a samu dan takarar da ya yi nasara ba wanda za a gudanar da zagaye na biyu a ranar 21 ga watan Fabrairun shekarar 2021, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.
“Makoka na kasa da kasa ko na mutum da mutum yana da matukar mahimmanci, wanda zaman lafiyar makocinka shi ne naka, haka kuma kwanciyar hankalinka shi ne na makocinka,” in ji shugaba Buhari.
Ya yi wa Jamhuriyar Nijar da Sambo da tawagarsa fatan alkairi na gudanar da zabe a karo na biyu a wannan mako.
Shugaban tawagar kungiyar ECOWAS ya bayyana cewa, an gudanar da yakin neman zabe cikin kwanciyar hankali da lumana kamar yadda tsarin jam’iyyun siyasan suka tanada.
A zaben farko dai, tsohon ministan harkokin waje, Mohamed Bazoum shi yake kan gaba da kashi 39.33 daga cikin kuri’un da aka jefa, yayin da tsohon shugaban kasa Mahamane Ousmane yake da kashi 17, wanda dukkansu babu wanda ya sami kashi 50 da zai ba shi damar lashe zaben a jikon farko.