Daga Abdullahi Abubakar, Lafia
A ci gaba da fadakarwa da yake yi wa jama’a su tare da jaddada musu bukatar da ke akwai na ci gaba da rungumar zaman lafiya a tsakani, mai martaba sarkin Lafia, Dakta Isa Mustapha Agwai na daya, ya yi kira ga al’ummar Migili da sauran al’ummomi da su hada kai su ci gaba da zaman lafiya da juna domin samun nasarori da kuma cigaba mai ma’ana ga Jihar Nasarawa da ma kasa baki daya.
Sarkin ya yi wannan kira ne sa’ilin da al’ummar Migili mazauna Lafia suka ziyarce shi tare da gabatar masa da sabon sarkinsu, wato Zhe Migili (Sarkin Kwarawa) na Lafia, Sunday Steben Kyari a fadarsa da ke Lafia.
Ya ce duk wani abin da al’umma ke nema na alheri ba ya samuwa sai da hadin kai, don haka tilas al’ummomi su hada kai domin samun biyan bukata.