CRI Hausa" />

Zaman Rayuwar Makiyayi Na Samun Kyautatuwa Matuka A Jihar Xinjiang

Gundumar Qitai yana arewa maso gabashin jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin. A shekarun baya-bayan nan, gundumar ta samarwa makiyayi gidaje 5732 bisa manufar zama dindindin da wadatar da makiyayi da kuma matakan gatanci na kawar da talauci da taimakon da birnin Fuzhou ke bata.
Tuo Han Kodabayi mai shekaru 60 ko fiye da haka dake zama a kauyen Jibuku na gundumar Jibuku na gundumar, ya ce, a da sun yi karancin karfin raya sha’anin kiwon dabobbi saboda ganin rashin hanyoyi masu kyau da karancin ruwan sha. Yanzu suna da gidaje na dindindin da dakunan kiwon saniya mai fadin muraba’in mita 200.
A halin yanzu, zaman rayuwar makiyayi na samun kyautatuwa matuka, gwamnatin ta baiwa makiyayi taimakon fasaha don kiwon dabobbi masu inganci.
Tuo Han Kodabayi ya ce, yana godiya sosai kan nagartattun manufofin da gwamnatin kasar ke dauka don taimaka musu. Alal misali, ya gina gidansa mai muraba’in mita 85, wanda ke da ruwan famfo da na’urar dumama daki da bayan gida da telibijin. Matakin da ya kyautata zaman rayuwarsu matuka, yana jin dadin zamansa a yanzu. (Amina Xu)

Exit mobile version