Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Luis Suares, ya bayyana cewa kawo yanzu zamansa a kungiyar ya kusa zuwa karshe kuma yana fatan kungiyar ta fara tunanin sayan dan wasan da zai maye gurbinsa.
Suares, wanda ya koma Barcelona a shekara ta 2014 inda ya shafe shekaru shida a kungiyar ya buga wasanni 173 inda kuma ya zura kwallaye 137 sai dai kawo yanzu dan wasan yana fatan kungiyar ta sami madadinsa.
A watan Janairu mai zuwa dan wasan dan kasar Uruguay zai kai shekara 33 a duniya kuma alamu sun nuna cewa kungiyar baza ta kara masa sabon kwantiragi ba wanda hakan yasa ya fara tunanin inda zai koma.
“Kasancewa a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ba abu bane mai sauki saboda duk bayan kwana uku sai anyi maka gwajin lafiya kuma duk lokacin da bakayi wasa mai kyauba zaka sha suka daga wajen magoya baya”
Ya cigaba da cewa “Akwai wahala buga wasa a Barcelona saboda da farko idan kai bako ne sai ka koyi abubuwa daban a kasar da kuma kungiyar sai dai ina godiya dana samu damar buga wasa a kungiyar kuma na gamsar da magoya baya.
A karshe ya ce idan kungiyar ta fara neman dan wasan gaba ba abin damuwa bane saboda yana fatan haka domin daman haka wasan kwallon kafa yake saboda nan gaba shekaru zasu hanani buga wasa yadda yakamata sannan kuma bazan iya gamsar da bukatar magoya baya ba.