Zamantakewa A Kasar Hausa Gabatarwa

Zamantakewa a nan na nufin yanayi ko tsarin zaman Bahaushe a al’ummance. Wannan kan-jawabi, wato Zamantakewa, darasi ne mai faɗi, wanda ya tattaro dukkan wani abu da za a iya faɗa game da yanayi da kuma tsarin yadda Bahaushe yake zamansa na rayuwar yau-da-kullum da ya shafi jagoranci da kuma cuɗanya tun daga ƙaramin mataki har zuwa Babba.
Tsarin zaman Bahaushe, cike yake da jagoranci da taimakon juna tun daga gida har zuwa kan sarki. Mafi ƙanƙantar yanki na zaman Bahaushe shi ne gida zaman mutum ɗaya; wanda yake da miji da mata su ne masominsa.
Wannan rubutu da mai karatu yake karantawa, zai yi magana ne iya bakin ƙoƙari game da zaman Bahauhse ta fuskacin iyali, jagoranci da kuma cuɗanya ta hanyar jeranto matsayin da mutane suke da shi daga na ƙasa zuwa na sama, tare kuma da siffanta irin gidajen da Bahaushe yake da daga ƙarami zuwa babba, sannan kuma da siffanta irin cuɗanyar Bahaushe ta fuskacin taimakon juna.
karamin Gida
karamin gida, shi ne yanki mafi kankanta a yanayin zamantakewar Bahaushe, shi ne gidan da yake dauke da miji da mata kawai; waɗanda kuma su ne tushe ko tubalin gina iyali. Yawanci a kasar Hausa a zamanin baya, ana samun irin waɗannan gidaje ne a cikin gandu.
Sannu a hankali irin wannan gida yake bunƙasa ya zama babban gida ko kuma gandu. Maigida, shi ne jagora a wannan gida.
Gandu
Gandu shi ne babban gida a Hausance. Shi kuwa babban gida shi ne gidaje a cikin gida. Gida ne makeke guda ɗaya wanda idan aka shiga cikinsa za a samu wasu gidajen, mafi ƙaranci guda biyu a cikinsa. Komai yawan jama’ar gandu, akan samu cewa tushensu ɗaya ne. Tushe a nan na nufin asali. Wato zuriya guda.
A irin waɗannan gidaje ake samun zuriya ko haula. Gida ne da ya tattara kaka, iyaye, baffani, yayye, ƙanne da kuma ‘ya’yan bafannin a guri guda.
Kowane gida guda ɗaya da yake cikin gandu, zaman kansa yake yi; da ma’ana ta yana da ɗakuna da kuma ban-ɗaki wasu lokutan ma da madafa a cikinsa. Kuma ana samun irin waɗannan gidaje a karkara har zuwa yau ɗin nan (28/9/2018) da nake yin wannan rubutun. Abin da kawai ya bambanta na daurin da kuma na wannan zamanin shi ne cewa, a yau za ka taras kowa a gidan gashin kansa yake ci. Amma da can baya kuwa, tukunya ɗaya ake ɗorawa.
Babban jagora a wanna gida shi ne namiji mafi yawan shekaru. Idan ya rasu; da ma’ana ta ya mutu, to mai binsa a shekaru, shi zai cigaba da jan ragamar gidan.
Dukkan sauran jama’ar gidan, sukan je gonar gandu su yi noma, sannan kuma su, mutanen gida, ana ware musu ranar Juma’a da kuma ƙarin wata rana wacce ita take zama ranar kasuwar garin, su riƙa zuwa tasu gonar suna noma wacce ake kiranta da gawaina/gayauna. Dukkan abubuwan da aka noma a gonar gandu, to shi za a riƙa dafawa a babbar tunkunyar gida. Idan aka samu tattaruwar irin waɗannan gidaje, sai su samar da unguwa.
Shi uban gandu, wato jagoran gida, shi ne alhakin kula da al’amuran ciki da wajen gida ya rataya a wuyansa. Shi ne mai bayar da aure a gidan sannan kuma shi ne mai karɓowa, shi ne mai sasanta tsakanin duk waɗanda suka samu saɓani a tsakani da sauransu. Maganarsa ita ce sama da maganar kowa a wannan gidan.
Unguwa
Haduwar daiɗaikun gidaje wadanda ka iya zama gandu ko kuma karamin gida, da yawa a waje guda shi ke samar da unguwa. Yawancin unguwannin Bahaushe musamman a karkara, sukan kasance ‘yan’uwan juna ne. Koda tushe bai zama ɗaya ba, auratayya takan haɗa wannan gidan da wancan.
Mai Unguwa shi ne yake shugabancin unguwa. Ana kuma naɗa mai unguwa ne a sabuwar unguwa ta hanyar la’akari da namiji mafi dattako da shekaru a unguwa. Daga kansa kuma sai abin ya zama gado.
Dagaci ne yake naɗa mai unguwa. Amma kafin naɗin nasa sai ya tuntuɓi sauran dattawan unguwa. Daga lokacin da aka naɗa wannan mai unguwa, shi yake zama wakilin dagaci a wajen mutanensa. Sannan kuma dai shi ne idon hukuma a wannan unguwa. Duk wata hulɗa da kuma isar da saƙonni da hukuma take son yi da jama’ar wannan unguwa, to ta hannunsa za a yi.
Akwai kuma nau’in unguwannin da ake kira kauye. Irin waɗannan unguwanni su ne gidaje ɗai-ɗai da suke a cikin daji.
Gari
Haduwar unguwanni da yawa a waje guda shi yake samar da gari. Shi kuma gari, dagaci ne yake jagorancinsa. Matsayin dagaci shi ne kamar matsayin kansila a yanzu.
Ana naɗa dagaci ne a matakin farko ta hanyar samun dattijo mai hankali daga cikin dattijan gari, wanda kuma jama’ar garin suke girmamawa, mai haƙuri da kawaici a naɗa shi a matsayin dagaci tare da goyon bayan sauran dattawan da ke wannan gari. Idan kuma wannan dattijo ya rasu, to sai ‘ya’yansa su gaje shi idan akwai. Dagan sarautar ta zama gado.
Dagaci shi ne idon hukuma a garinsa. A duk lokacin da hukuma take son yin hulɗa da jama’ar garin baki ɗaya, to ta hannunsa ake bi, shi kuma sai ya miƙa saƙon zuwa ga masu unguwanninsa.
Gunduma
Gunduma yanki ce da ta tattara garuruwa, kauyuka da unguwanni daban-daban a karƙashinta. Ana kiranta kuma da ƙasa, saboda kasancewarta yanki mai faɗi. Hakimi shi ne ke jagorancin gunduma. Gunduma ita ce kwatankwacin ƙaramar hukuma a yanzu. Matsayin hakimi kuma shi ne kamar matsayin shugaban ƙaramar hukuma wato ciyaman.
Wannan kujera ta hakimi kuwa ba a gadonta. Sarki ne yake naɗa wanda ya so daga cikin ‘ya’yansa da kuma makusantansa. Shi hakimi yana wakiltar sarki ne. Shi kuma dagaci ya wakilce shi, dagaci kuma ya wakiltar da mai unguwa.
Hakimi shi yake zama idon hukuma; wato wakilin sarki a gudunma. Dukkan wani saƙo da sarki yake son isarwa ga jama’a, zai fara tura shi zuwa ga hakimai, su kuma su turawa dagatai, dagatai kuma su turawa masu unguwanni, su kuma kodai su isar da shi kai tsaye ko kuma su isar da shi zuwa ga shuwagabannin gandu. Ya danganta da wane irin sako ne.

Exit mobile version