Zamantakewa Da Cudanyar Hausawa Da Sauran Al’ummomi

Hausawa

Hausawa ma al’umma ce mai yado wadda ita ma ta tana da irin wannan zaman na daga ni sai iyalina kamar yadda muka ambata a baya. Hakazalika, Hausawa suna da kafaffiyar al’umma mai ‘yancin walwala da na gudanarwa ta yadda mutanenta sukan fita don neman abin hannunsu Wajen gudanar da sana’o’i daban-daban. Irin wadannan tafiye-tafiye ne suka kai Hausawa wasu wurare nesa da kasarsu ta haihuwa a lokuta daban-daban. Baya ga haka, mafi yawancin mazauna kasar Hausa al’ummar Hausawa ne, amma akwai wasu kabilu wadanda suka yi kaura ko hijira daga garuruwansu wanda a yau wasunsu sun koma Hausawa a harshe da al’ada da ma adabinsu, wadannan irin kabilu sun hada da Fulani da Buzaye da Barebari da Nufawa da Yarbawa da sauransu.

Don haka, sanadiyar wannan kaura da magabatansu suka yi zuwa kasar Hausa sun manta da harshensu da adabinsu da al’adunsu na asali sun dauki na Hausawa kamar yadda muka ambata a baya. A takaice, sun koma Hausawa a harshe da adabi da al’ada.

Dalilan Da Suka Haifar Da Cudanyar Hausawa Da Sauran Al’ummomi Sun Hada da:

 1. Kaurace-kaurace
 2. Fatauci
 3. Yake-yake
 4. Laura, ita ce motsin mutane da kayansu da wani waje zuwa wani. Don haka, Hausawa sun yi Laura zuwa wadansu yankuna ko kasashe kamar yadda wadansu kabilun suka yo kaura izuwa kasar Hausa. Dalilan wadannan kaurace-kauracen akwai, bore saboda bauta, ko saboda tursasawar da wasu sarakunansu na kasar Hausa suke yi musu da kuma don guje wa hukuncin mahukunta a dalilin wani laifi da suka aikata. Wasu kuwa sun yi kaura ne don ra’in Kansu. Haka kuma wasu Hausawa suna tafiya tare da ayarin fatake don su yi yawon almajiranci da yada addinin Musulunci a kasar da Hausawa suka sauka a yawancin zanguna da ke a kasashe wadanda ba na Hausawa ba, sun kasance suna koyar da ‘ya’yan fatake da mazauna a can ko da yaushe. A cikin garuruwan da Hausawa suka yi kaura izuwa wadancan wuraren akwai irin su Neja, da Kudancin Kaduna, da Lafiyar Barebari da Lokoja da Badun, da wasu kasashe da suka hada da Ghana, da Afirka ta Tsakiya da Sudan da dai sauransu.
 5. Fatauci, Hausawa suna shirya fita fatauci na wasu kayayyakin masarufi da dabbobi kamar tumaki da awaki da jakuna da bayi da sauransu. Duk da cewa an sami wasu kasuwani masu girma a kasashen da ba na Hausawa ba, kamar kasar Nufawa, da Lokoja da Fulato da Lafiya Badun da Kurmi (Legas) da ma Gwanja (Ghana) da Afirka ta Tsakiya da dai sauransu.

An gudanar da wannan fataucin ne a lokacin baya, Wanda an fi aiwatar da wannan fatauci a lokuta daban-daban ba ma kamar a lokacin kaka. Saboda haka, harkokin mutane sun inganta ta irin wadannan hanyoyi. An sami habakar fatauci ne a zamanin Sarkin Kano Abdullahi Burji(1438-1452) Wanda ya rinka daura yaki yana kamo bayi da yawa daga kudancin kasarsa. An ce a wani lokaci sai da ya kamo bayi har dubu ashirin da data(Lobejoy, 1980:52). Sannan ya rarraba su a wurare 21 a cikin Kano. A dai lokacin ne aka rinka samun abin sayarwa Wanda har daga kasashen waje ake KAWO goro da garin zinari zuwa Kano, sannan kuma ana tafiya da bayi. A dai zamaninsa ne kasuwar kurmi ta rinka Samar da kayayyakin ciniki daga kasashen duniya.

 

Ire-iren kayan da aka fi yin fataucinsu a wancan lokacin daga kasar Hausa zuwa makotansu, ko kuma daga makotansu zuwa kasar Hausa.

 1. Fataucin goro
 2. Cinikayyar bayi
 3. Kayan abinci
 4. Tsakiya
 5. Fatu
 6. Darma da tagulla da garma da fartanya da dai sauransu.

Akwai sauran kayayyaki na karau da kwalliya da aka yi fataucinsu daga kasar Hausa zuwa sauran kasashe ko kuma daga wadansu yankuna zuwa kasar Hausa. Wannan cinikayyar ta haifar da cudanyyar Hausawa da sauran al’ummomi na makwabta da sauran kasashen Afirka da ma kasashen duniya.

A wancan lokacin, cinikin ana yin sa ne ta hanyar ba-ni-gishiri-in-ba-ka-manda, musamman matan kere-kere da na saki a wajen karni na 15 da na 16(Shu’aibu 2011:87).

Hausawa A Wasu Kasashe.

Shu’aibu(2011:79) a makalarsa dake “Algaita” ya bayyana cewa, Hausawa sun yi yawace-yawace zuwa wasu kasashe nesa da tushensu wato kasarsu. Wasu daga cikin kasashen sun hada da:

 1. Kasashen Larabawa
 2. Kasashen Turai
 3. Afirka Ta Arewa
 4. Afirka Ta Yamma

Mene ne ya kai su?

Auwal Abdullahi Salisu, Kano

 1. Zamantakewa

 

 

Exit mobile version