ZAMANTAKEWA: Shawara Daukar Daki

Da yake yaki dan dabara ne matukar dai ana so a yi nasara, to baya ga ba da karfin gwiwa cikin yin imani da jajircewa, to akwai kuma shawara (wadda masu hikimar magana suke yi wa kirari da shawara daukar daki). Batun na ji ko daukar shawara shi ne kuma maudu’in tattaunawar tamu ta yau, a ci gaba da tsokaci cikin matakan yakar damuwa. Hasali ma, ita damuwa ai mugunyar halayyara nan ce da kan yi wa shu’aunin rayuwarka dabaibayi har ka kasa yin katabus balle kuma ka samu tudun dafawa.

Sau da yawa za ka ga mutane cikin matsanancin bakin ciki, har suna bayyana kukansu domin neman samun taimako daga Ubangijin daukaka da buwaya. A kowane  lokaci muna bukatar taimako, to amma kuma mun fi so Allah (SWT) ya yi mana ta son ranmu, shi kuma ya fi ganin dacewarta cikin zabi da tsarinsa. Gaskiyar maganar ita ce, duk irin yadda muke bukatar taimako, to fa ba zai samu ba face muna daukar shawara dangane da yadda za mu inganta rayuwarmu. Wato ka samu fahimtar gaskiya a duk lokacin da za ka gabatar da wani lamari da ya shafi rayuwarka.

Wajibi ne ka zamo kana da tsari ko hanyoyi na tafiyar da rayuwarka, kuma ka tabbata idan aka bi su wadannan tsare-tsare za a samu nasara. Amma kuma sau da yawa garajenmu kan jefa mu cikin matsaloli iri daban-daban. Ga misali, sau da yawa mukan shawarci dalibai da su kasance nagari, wato wajibi ne su kasance masu zage damtse da yin karatu tukuru a koda yaushe. Idan kuwa ba haka ba, to ba za su samu nasara da daukaka ba. Sau da yawa din kuma daliban kan bayyana mana irin mawuyacin halin da suka shiga domin neman shawara, idan kuma suka ki ji to ba sa ki gani ba. Ba a kowane lokaci ma hakan take faruwa ba, to amma kuma ai taya Allah kiwo ya fi Allah na nan! A gaskiya ma, kamata ya yi mu kasance cikin rayuwa mai inganci, cikin kwanciyar hankali da lumana da kuma zaman lafiya. Da yake zama ne na cude-ni-in-cude-ka, to mu rika yafe wa juna idan sabani ya auku a tsakaninmu. Saboda haka, matukar ba mu dauki shawara muka yi abin da ya kamata mu yi ba, to sakamakonmu na garemu.

Idan kuma muka aikata abin da ya kamata kuma ya dace, to Allah (SWT) yana tare da mu, cikin jibintar al’amuranmu. Na lura dalilin da ya sa ba mu cika aikata abin da ya dace ba shi ne, rashin daukar shawara cikin shu’unin rayuwarmu. Ashe babu laifi tuntubar juna dangane da wata damuwa da ta bijirowa wani ko kuma wasu a cikin al’umma. Ta haka ne za a shawarta da juna har a samo bakin zaren maganin wannan damuwa. A wasu lokuta ma akan yi gamo da katar cewa irin halin da wani ya shiga, to wani ma ya taba samun kansa a ciki, kuma ga yadda aka bi har aka samu maslaha. Ta wannan haujin, shawara ta yi tasiri.

Akwai kuma batun fada da cikawa, wato bibiyar tsarin da rayuwa ta tanada da kuma bi sawu da kafa. Na tuna wata mata mai jimirin karatun filin ‘Zamantakewa’, da ta yi fatawa dangane da wata matsala da ta dade a cikinta. Ita dai tana fama da matsananciyar damuwa ne, da har takan sanya ta fargaba da kuma jin tsoro. Kwarai ta so ta samu ‘yanci na rabuwa da wannan halayya, to amma komai ya ki tafiya yadda take so. Bayan mun tattauna kuma na ba da shawara, sai ta bayyana cewa ta fahimci dalilin da ya sa babu wani ci gaba a lamuranta. Ta ce ta yi mu’amala da wasu mata masu kwatankwacin matsalarta a shekarun baya, kuma sun yi fama da matsananciyar damuwa har sannu a hankali suka samu sauki.

Bayan ta saurare su, ta tuna suna cewa Allah (SWT) ne ya kawo mana sauki sannu a hankali cikin shawarwarin da muka samu. Daga nan ita ma sai ta rika jin kamar ana ce mata ita ma ta dauki sahawarawari daga wajen sauran mutane dangane da matsalarta. Ta ce bambancinsu da ita kawai shi ne, su sun aikata duk abin da ya  kamata (wato fada da cikawa cikin shu’unin rayuwarsu), ita kuwa ba ta yi ba kuma hakan ne dalilin tsanantar tata matsalar. Idan da so samu ne, to da kamata ya yi duk wanda aka ba shi shawara ya kasance mai fada da cikawa. Sai dai kuma da yake komai aka yi da jaki sai ya ce kara, za ka samu cewa wasu mutane ba sa so su warke (ko kuma su rabu da matsalar damuwarsu), a maimakon haka sun gwammace su yi yadawa a cikin al’umma cewa suna da matsala. A gaskiya gardama da gajen-hakuri ba sa fitar da mutum daga cikin wani kangi da ya samu kansa a ciki, har sai ya shawarta domin ita shawara daukar daki ce!

tare da Farfesa Salisu A. Yakasai

08035073537, 08154615357 (Tes kawai)   Syakasai2002@yahoo.com

Exit mobile version