Tare Da Fasto Yohanna Y.D. Buru
0806 871 8181
Jama’a muna kara godiya ga Ubangiji Allah Makadaici, Mai girma, marasa farko balle karshe, Mai kowa da komai, wanda kuma Shi ne kadai Mai daukaka har Abadah abadi, Amin. Godiya ga wannan Jarida mai daraja da kuma tsaga gaskiya daidai gwargwado, muna godiya mai yawa zuwa ga dukkan ma’aikatanta da wannan zarafin da kuka ba mu domin yin Bishara ko idar da sakon Allah ga mabiyan addinin Kiristanci ga iKristocin duniya gaba daya, wato masu jin Hausa. Mun gode matuka.
A cikin zamantakewar Krista da kowane irin mutum, ko danuwarsa, Kirista ne ko makwabcinsa Musulmi ne ko kuma wasu Mabambantan addinai. Littafin Mai tsarki ya dauki lokaci mai yawa domin ya koya wa Kiristoci halayyar kyakyawar zamantakewa da kowane irin mutum akan wadanan dalilai.
- Domin Kirista na da makwabta
- Kirista na zaune tare da mabambantan addinai
- Kirista na zaune tare da mabambantan akidu
- Kirista na zaune tare da wasu kabilu
- Kirista na zaune tare da wasu jinsin mutane
- Kirista na zaune tare da makiyansu ko masu tsananta masu da ire-irensu.
- Kirista na zaune tare da Kafirai/Arna
- Kirista na zaune tare da wadanda suna musu da cewa akwai Allah.
Da wadannan dalilai da wasu da ba mu ambata ba, su ne Allah Ubangijinmu ya koyar wa Kirista halin zamantakewa da kowanne irin mutum.
A wadannan ayoyin, wato bb13-14, Allah Ubangiji ya fara da koyar wa Kristoci mu’amula ne tsakanin Kirista da dan uwansa Kirista. Domin in Kirista bai san yadda zai yi mu’amala da kuma kyakyawar zamantakewa da dan uwansa Kirista ba, to ta yaya ne zai iya yin kyakyawar mu’amula har kuma ya kyautata zamantakewarsa da wasu mabambantan addinai?
A aya ta b13 mun karanta cewa Kiristoci: “Kuna rarraba dukiyarku zuwa biyan bukatar tsarkaka; kuna rika yin gyaran baki.”
Babu yadda za mu iya gane da fassarar wannan ayar, ba tare da mun koma a aya ta b 10 da ke bisa ba. “Ku yi zaman dadin soyayya da junanku cikin kamnar ‘yan uwa; kuna gabatar da kuna cikin ban-girma.”
A nan ana nufi da cewa; babu yadda wani zai dauki dukiyarsa har a rabar wa juna sai da cikakiyar zaman dadin soyayya. Wanda ka ke kauna, shi ne za ka so ka taimake shi a cikin kowane hali. Masu iya magana sun ce; ‘kayan so ba shi da nauyi.’
Matuka Kiristoci suna cikin dadin zaman soyayya da juna kuma a cikin kamnar juna, to rarraba dukiyarsu ga juna abu ne mai sauki. Domin soyayya da kaunar ko kamnar juna zai ingiza su zuwa ga rarraba wa juna dukiyarsu, ba tare da wata mishkila ba.
Babu wanda zai iya daukar dukiyarsa ya rabar wa makiyinsa sai dai Kirista ne da Ubangiji Allah ya umurce shi da ya yi haka. Watakila ga hikimar da ke kunshe a cikin wannan umurnin da Ubangiji Allah ya baiwa Kiristoci, da su fara kyautata zamantakewa tsakanin su da juna, domin ta wurin haka ne za su kwaikwayi yadda za su yi wa makwabtansu har ma da makiyinsu ko masu tsananta masu: (Marta 5:44-45; Romawa 12:20).
Kama yadda muka fada a jawabinmu na baya da cewa addinin Kirista tushensa ko assalinsa ta kafu akan kamna ko kauna ne. Kuma addinin Kirista ba ya ci ka in dai ba tare da kyakyawar zamantakewa da mu’amula da kowanne irin mutum ba.
Ana iya gane cikakken Kirista ta wurin halayyarsa nagari ko halaye kyawawa. Cikakken Kirista ana gane shi ta wurin kaunar ko kamnar da ya ke nuna wa dan uwansa Kirista, makwabcinsa, makiyinsa da mai tsananta masa. Uwa uba shi ne, irin kyakkyawar mu’amularsa da zamantakewarsa da kowanne irin mutum, da kuma ta wurin kauna ko kamnar da yake nuna wa kowane irin mutum, shi ne alamar cewa wannan cikaken Kirista ne.
Umurnin rarraba dukiyarsu shi ne, domin akwai mabukata a cikin Kiristoci da kuma makwabta ko mabambantan addinai. Rabon dukiya tsakanin su da juna wata manuniya ce da cewa in sun iya yi wa junansu haka, to haka ma za su iya yi wa makwabtansu domin su nuna wa juna da makwabta kaunar ko kamnar Almasihu da koyarwarsa.
Wato, abin da muke nufi a nan shi ne, a cikin littafin Romawa 12:20 an umurci Kiristoci da su kwatanta wa makiyinsu alheri a lokacin da suna jin yunwa ko kishi. Aya ta tabbatar mana da cewa: “Amma idan makiyinka yana jin yunwa, ka cece shi; idan yana jin kishi, ka ba shi sha; gamagarin yin haka, za ka tara masa garwashin wuta akansa” (Romawa 12:20).
To don Allah, in Allah ya umurci Kirista da ya yi wa makiyinsa alheri duk da tsakanin kiyayyan da ke a kunshe tsakanin su, balle tsakanin Kirista da Kirista fa? Babu mamaki, da Allah ya umurci Kiristoci da su rarraba dukiyarsu ga juna domin su inganta mu’amularsu da juna, domin ta haka ne za su iya yi wa makwabtansu alheri a ta kowane hali.
Wannan ita ce tushen kyautatuwar mu’amula da zamantakewa tsakanin Kirista da Kirista, da kuma tsakanin mabambantan addinai, ko da makwabcinsa har ma da makiyinsa.
A aya b13b an umurci Kiristoci da cewa; “…kuna rika yin gyaran baki.” Gyaran baki a cikin addinin Kirista umurni ne domin albarkatun da ke kunshe a cikin yinta. A Littafin Ibraniyawa, marubcin ya tunatar da Kiristoci akan cewa: “Bari kamnar ‘yan uwa ta lizima. Kada a manta a nuna kamna ga baki: gamagarin yin wannan, wadansu sun saukar da Mala’iku ba da saninsu ba” (Ibraniyawa 13:1-2).
To ko ma ba tare da albarkar da ke kunshe a cikin gyaran baki ba, ai saukar da Mala’iku wata babbar ni’ima ce da wata dama da ba kowane mutum zai iya samun ta ba. Wannan ni’ima na samuwa ne ta wurin ilimin kyakkyawar mu’amula da zamantakewa ne kadai za a iya samun damar saukar da Mala’iku.
In mun koma a aya ta b14 za mu karkare tattaunar mu a yau.”Ku albarkaci wadanda ke tsanarta ku; ku albarkace su, kada ku la’anta.”
A cikin halin kyakyawar zamantakewa da mu’amula da makiyinsu Kirista, Allah na umurtar Kirista ko Kiristoci da su albarkaci wadanda ke tsananta masu.
Jama’a masu karatu, muna maku fatan Alheri. Allah ya albarkace ku cikin sunan Yesu Almasihu, Amin.