Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home FAHIMTA FUSKA

Zamantakewar Kirista Na Nan A Cikin Littafi Mai Tsarki (Bible)

by Tayo Adelaja
September 17, 2017
in FAHIMTA FUSKA, NAZARI
4 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Tare Da Fasto Yohanna Y.D. Buru yyohanna@gmail.com

Ga Sura da Ayoyin: Romawa 12:9-21.

Wannan Sura ta bayana mana yaya Zamantakewar Krista take, wato tsakanin Kirista da kowanne irin jinsin mutane. Mafi muhimmanci a cikin koyarwar addinin Krista shi ne ‘Kauna.’ Kuma Manzo Bulus ya dauki lokaci ya bayana wa masu bin addinin Kirista muhimmancin kauna ita ce cikon addini.

Wannan koyarwa na samuwa a Littafin 1 Korinthiyawa 13:1-8, a cikin wannan surar ta bayyana mana muhimmanci kauna har da ma in Kirista ba shi da kauna, to ba zai gaji mulkin Allah ba.

In mun koma ga Littafin Romawa 12:9-21, za mu iya gani da aya 9 a cikin Romawa 12 shi Manzo Bulus ya Fara da cewa: “Bari kamanta zama ba tare da riya ba. Ku yi kyamar abin da ke mugu; lizimchi abin da ke nagari.”

Wannan ayar tana koyar wa Kirista da ya zama mai kamna ko kauna ya ba kowanne irin mutum, ba tare da riya ba. Littafin Ibraniyawa 1:9 ta tabbatar da wannan maganar kamar haka: “Ka yi kamnar adalci, ka ki mugunta; Domin wannan fa Allah, Allanka ya shafe ka Da man farin ciki gaba da tsararakinka.”

Kamna ko kauna a cikin addinin Krista ita ce ma’aunin komai, Kirarin bin addinin Krista na da ita ko babu. A takaice, kamna ko kauna ita ce ma’aunin Kirista na gaskiya.

Duk cikaken Kirista in ba shi da kauna ko Kamna, to ba cikaken Kirista ba ne. Kuma matukar Krista ba shi da kauna ko kamna, to babu yadda zai iya bauta wa Allaasa, ba kuma zai taba iya kyakkyawar zamantakewa ba. Domin in babu kamna ko kauna, to kirista ba cikakken ikon kyakkyawar mu’amala da Kiristoci ko mabambantan addidinai.

Ikon kauna ko kamna ne kawai za ta iya taimakon Krista har ya iya kaunaci ko kamnaci makiyinsa ko kuma ya yi wa maitsananta masa addu’a. Ga abinda Yesu Almasihu ya koyarwa masu binsa:

“Kun ji aka fadi, Ka yi kamnar makwabcinka, ka ki magabcinka: amma ni ina ce maku, ku yi kamnar magabtanku, kuma wadanda sukan tsananta maku, ku yi masu addu’a.” (Matta 5:43-44).

Daga wadannan ayoyi, kowa zai gane sai dai ta wurin kauna ko kamna ne kawai Krista zai iya kyakkyawar mu’amala da Zamantakewar da kowanne irin mutum.

In mun koma ga Littafi Mai tsarki, a cikin 1 Koronthiyawa 13:1-8, za mu tarar da gaskiyar maganar cewa kauna ko kamna ita ce sinadarin Zamantakewar da kuma kyakkyawar mu’amala tsakanin Kirista da kowanne irin Mutum. Bari mu duba Ayoyin nan Kamar haka:

“Kamna tana da yawan hakuri, tana da nasiha, kamna ba ta jin kishi; kamna ba ta yin fahariya, ba ta yin kumbura, ba ta yin rashin hankali, ba ta bi da makanta, ba ta jin cakuna, ba ta yi nukura, ba ta yi murna cikin rashin adilci, amma tana murna da gaskiya; tana kafa bege ga abu duka, tana daurewa da abu duka. Kamna ba ta karewa da dai sauransu;……. “(1 Korinthiyawa 13:4-8).

Kamar yadda na fada tun daga fari, cewa kauna ko kamna ita ce sinadarin kyakkyawar zamantakewar da kuma kyaykyawar mu’amala. To ga shi nan dai Manzo Bulus ya kara tabbatar mana a cikin maganar Allah, wato Littafi Mai tsarki. Allah ta wurin Manzonsa ya lissafa mana kyawawan abubuwan da kauna ko Kamna ke iya yi, amma ga wanda ke da shi.

Littafi Mai tsarki ya tabbatar mana da cewa kauna ko kamna ita ce alamar halayyar cikaken Kirista. Domin haka duk wanda ke da kauna ko kamna zai iya aiwatar da ayyukan kamna ko kauna.

A tuna fa, mun gani Littafin Mai tsarki ya bayana mana cewa kauna ko kamna tana hakuri. To in kamna ko kauna tana yawan hakuri, to ai mahakurci mawadaci, in ji masu iya Magana! Hakuri shi ne gishirin zaman duniya. Duk mai hakuri zai iya zama da kowanne irin mutum, ya kuma ci gaba da kowace irin mu’amala ko kyakkyawar Zamantakewarsa. Mai hakuri zai iya zaman lafiya da kowanne irin mutum, komin bambancin al’ada, kabili, yare, jinsi, addini da kuma kowanne irin bambanci.

Kuma ko kauna na da nasiha, in akwai nasiha, to akwai ci gaba, zaman lafiya. Kauna kuma, girmama juna da mutunta juna. Kamna ko kauna ba ta jin kishi, to ai in babu kishi tsakanin juna, to ba za a yi wa juna ha’inci ba, ko zalunci, ko munafunci, ko hassada. In kuwa kauna ba fahariya, to za a sami al’umma nagari masu tawali’u da gaskiya da kuma rashin tsangwama.

A takaice, in za mu dauki lokaci mu yi nazari ko zurfin tunani tawurin kwatanta Littafin Romawa 12:9 da 1 Korinthiyawa 13:4 za mu gane cewa kauna ko kamna ba ta tare da riya.

A takaice in mun koma ga Littafin Romawa 12:9 da 1 Korinthiyawa 13:4, in mun yi kyakkyawar nazari ta wurin kwatanta wadanan ayoyin nan guda biyu za mu koyi abubuwa masu yawa.

Romawa 12:9 ta nuna mana cewa kauna ko kamna a cikin halin zamantakewa a bari kauna ta zama ba tare da riya. Wato kauna in dai na gaskiya ne, to ba ta riya, amma tsakani da Allah ne. kauna ko kamna ba ta san da munafunci ko mugunta ba, sai dai alheri.

Kauna ko kamna ba ta cutarwa sai dai kyautatawa. kauna ko kamna na kyamar mugunta sai dai alhairi da kyakkyawar ma nufa. In akwai kauna ko kamna, to akwai kyakkyawar mu’amula da kyautata juna. In akwai kauna ko kamna, to al’umma za su karu ta wurin ci gaba. kauna ko kamna na inganta kyakkyawar mu’amala da kyakyawar zamantakewa.

Kauna ko kamna ne ke sa Kirista ya lizimta a cikin abin da ke nagari. Zamantakewan Kirista tana kafuwa ne a turbar kauna. Kaunar da ke zuciyar Kirista shi ne ke ingiza shi ga kaunar makwabcinsa kamar kansa, ko addinin su daya ko ba daya ba. Kuma kauna tana da yawan hakuri. Duk Wanda Allah ya albarkace shi da yawan hakuri, to tabbatace zai gama lafiya da duniya, ko zai zama mai sada zumunci da kowanne irin mutum, kamar yadda Yesu Almasihu ya umurci Kristoci su yi a Littafin Matta 5:9.

Duk mai yawan hakuri tabbas shi mai nasara ne cikin komai. kauna ko kamna tana da nasiha. Duk mutumin da ke da nasiha, to kyakkyawar mu’amala kuma mai nasiha mai kyakkyawar zamantakewa ne. Kauna ko kamna ba ta jin kishi. In babu kishi, to akwai kyakkyawar zamantakewa a ko’ina, in kuma akwai kyakkyawar Zamantakewa, to tabbas akwai zaman lafiya da ci gaba a kowanne fannin rayuwar bil Adama.

Kauna ko kamna ba ta fahariya ko kumburi. In Kiristoci sun zama marasa fahariya da kumburi, to Ekkilisiyya ko al’umma Kirista za su zama masu albarka da misali ga jama’a.

Za mu tsaya a nan, sai mako na gaba. Ku zama da albarka cikin sunan Ubangijinmu.

SendShareTweetShare
Previous Post

Labarin Bawa Dorugu: Bahaushen Farko Da Ya Fara Zagaya Turai

Next Post

Babban Darasi Ga Dattawa, Sarakuna Da Shugabannin Igbo

RelatedPosts

Tarbiyyar ‘Ya Mace A Zamanance

Tarbiyyar ‘Ya Mace A Zamanance

by Sulaiman Ibrahim
3 days ago
0

Daga A'isha Muhammad A wanna Mukalar zan yi duba ne...

Lokaci

Muhimmiyar Tsaraba Ga Ma’auratan Jiya Da Na Yau

by Sulaiman Ibrahim
3 days ago
0

Daga Yusuf Kabir Aure yana daya daga cikin abin da...

Maleriya

Yaushe Za A Samar Da Riga-kafin Maleriya A Nijeriya?

by Muhammad
1 week ago
0

Daga Najeeb Maigatari, A rubutun da ya gabata na dan...

Next Post

Babban Darasi Ga Dattawa, Sarakuna Da Shugabannin Igbo

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version