Connect with us

JAKAR MAGORI

Zamfara Da Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Kashe 15 A Sabbin Hare-hare

Published

on

‘Yan bindiga sun kashe mutum 15 a Unguwar Yabo cikin kauyen dake yankin karamar Hukumar tsafe ta Jihar Zamfara, da yankin karamar Hukumar danmunsa ta Jihar Katsina.

Mutum 12 ne aka kashe a harin da aka kai Zamfara, yayin da aka sake kashe mutum uku a jihar Katsina.

Wani dan asalin kauyen, Malam Sani Mohammed, ya fadawa PUNCH Sunday cewa, maharan sun mamaye kauyen akan babura inda suka fara harbin mutane ba babu kakkautawa.

Muhammed ya ce, ‘yan bindigar sun shafe awonni a cikin kauyen suna harbe-harbe gami da satar dukiyoyin mutane ba tar da kawo wani dauki daga jami’an tsaro na yankin ba.

A bangaren kisa kuwa, Muhammed ya ce, mutane da dama sun samu munanan raunuka na harbi da bindiga.

“ Mun ga wuta da idanunmu, wadannan miyagun marasa zuciya sun lalata kauyen, saboda mafi aksarin mutanen da aka kashe 12 da wadanda aka yi wa munanan raunuka duk mutanene da muke alfahari da su,” in ji shi.

Muhammed ya kara da cewa, shi ma ya yi sa’ar tsira da ransa yayin da tsere zua cikin jeji a kokacin da ake ta harbe-harben, amma ya ce, wansa Ibrahim na daga cikin mutanen da ‘yan bindigar suka hallaka.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Jihar Zamfara, SP Mohammed Shehu, ya tabbatar da afkuwar lamarin, amma a cewarsa mutum hudu ne kawai suka rayukansu.

Shehu ya ce, da yawa mutanen da suka samu raunuka an tafi da su izuwa babban asibitin Tsafe domin basu kulawa.

A harin na Katsina, ‘yan bindiga sun ba da tsoro a kauyen Marar-Zamfarawa, inda aka ba da rahoton kashe mutane uku da raunata wasu uku.

An bayyana sunayen wadanda suka rasa rayukansu kamar haka; Aminu Yusuf, Lawal Akushi da Mansir Danliti. wadanda aka jikkata kuma sun hada da; Rabiu Mala, Shamsu da Sharhabilu, wadanda a halin yanzu suna babban asibitin Danmusa suna karba magani.

An gano cewa wadannan ‘yan bindiga sun aiwatar wannan hari ne a tsakiyar dare bayan sahu ya dauke.

Rahotanni sun nuna cewa, rundunar jami’an tsaro da wasu yan sintiri sun kai dauki yankin, lamarin da ya sa maharan su koma zuwa daji.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce mutum biyu suka rasa ransu a wannan harin.

Ya kara da cewa, “An binne mutanen da suka mutu a safiyar ranar Asabar,” in ji shi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: