M.U Abubakar" />

Zamfara: Rana Ta Fito Gari Ya Waye (1)

Gab da za a rantsar da wadanda Allah ya ba su nasarar lashe zabe a zabukan da suka gudana a Najeriya cikin watan Fabrairu da Mayu, kwatsam hukuncin babban kotun koli ya sauya al’amura a jahar Zamfara, sakamakon kwace haramtacciyar nasarar jam’iyyar APC, tare da mika sahihan takardun tabbatar da nasara ga dan takarar jam’iyyar PDP.

Babu bukatar dogon bayani game da halin da al’ummar Zamfara suka tsinci kansu tsawon shekaru hudu na mulkin Abdul’Aziz Yari. Duk wani dan asalin jahar kullum kuka yake yi sakamakon irin tarin bakin ciki da suka tsinci kansu a ciki ta dalilin ci bayan da jahar ke ta samu ta fuskar tattalin arziki, tsaro, ilmi, lafiya, walwala da sauran su. A takaice, za a iya cewa babu wani sashe da yake aiki yadda ya kamata a jahar.

Al’ummar jihar Zamfara ba za su taba mantawa da lokacin da daruruwan ‘yan Najeriya suka fita kan tituna a wasu jihohi na kasar da ma Abuja, inda suka rika  yin kira da babbar murya tare da nuna fushinsu da damuwarsu kan kashe mutane da ake yi a jihar Zamfara.

Mutane sun sun rike kyallaye masu rubutu daban-daban na nuna fushinsu kan abin da suka kira kisan gillar da ake yi wa mutane, da kuma kunnen uwar shegu da hukumomi suka yi a kan lamarin, musamman shi kansa gwamnan da zama a jahar tasa ma ya gagare shi.

A shafin twitter an yi ta amfani da maudu’ai har kala uku da suka hada da #MarchForZamfara #SabeZamfara da kuma #ZamfaraIsBleeding.

Mazauna kauyuka sun shiga mumman tashin hankali, kullum cikin kai musu hari tare da yi musu yankan rago ake yi. Wasu kuma a sace a bukaci makudan kudade. A hannun Abdulaziz Yari, tsaro ya tagayyara, rayuka sun salwanta, asarar dukiya ba a magana; amma ba za a iya nuna wani kwakkwaran kokari da ya yi wajen dakile matsalar ba, a matsayinsa na babban mai kula da tsaro na jahar.

Tsohon Sanata daga Zamfara, Sanata Kabiru Marafa, ya taba bayyana cewar akalla akwai yara sama da 110,000 (dubu dari da goma) wadanda suka rasa iyayen su ta dalilin hare-hare, suna nan suna garambaba, babu abinci, babu wurin kwana. Yayin da tsohon gwamna yake Abuja yana yawonsa a fadar Shugaban kasa.

Ilmi ya dade da shiga mummunan hannu a Zamafar, kai ka ce ma al’ummar jihar tsoron sanya ‘ya’yansu a makarantar suke yi. Babu shakka, idan iyayen ‘ya’ya sun ji tsoro sam ba su laifi ba, domin gwamnatocin baya sam ba su bawa hakan muhimmanci ba, balle al’umma su yarda da su.

A shekarar bara kasa da dalibai 60 suka rubuta jarabawar shiga makarantun hadi kai guda 104 da muke da su mallakin gwamnatin tarayya, yayin da a jihar Legas kadai, dalibai 25,000 (dubu ashirin biyar) ne suka rubuta. Wannan ya kara bayyana karara irin tashin hankali da matsalar ilmi ke fuska a jihar bisa sakacin gwamnati.

Kididdiga ta nuna daga ofishin Kula da Ilmin Yara na Majalisar Dinki Duniya, wanda wakilinsu na Sokoto, Mohammed Fall ya bayyana, ya nuna cewar a shekarar 2016, a karamar hukumar Bukkuyum kadai akwai yara 93,849 (dubu casa’in da uku da dari takwas da arba’in da tara) da ba su zuwa makaranta, mafi yawancin kuma mata ne.

A karamar Hukumar Maradun yara 63,943 (dubu sittin da uku da dari tara da arba’in da uku) ba su kai ga matsayin da gwamnati za ta kula da su har ta sama musu ilmi ba. Karamar hukumar Zurmi ma haka abin yake, sama  da yara dubu 80 ba su zuwa dakin karatu. Kullum adadin karuwa yake yi, saboda gwamnati ba ta yi tsarin da matsalar za ta ragu ba.

Allah ya yi wa kasar Zamfara arzikin ma’adanai fiye da wasu manyan jihohi a Najeriya, mafi muhimmanci ma shi ne kasar noma, mai girma, wadda da shugabanninta da suka gabata sun yi aikin kwarai, babu mamaki yanzu ta rika gogayya da sa’o’inta ta fuskar ci gaba.

Duk da cewa gwamnatin Tarayya kadai ke da ikon hako ko sarrafa ma’adanai irin su zinare da tagulla, tama da karafa, hakan bai hana gwamnatin jiha neman lasisi ko izni ba. Babu wanda ya hana gwamnatin jiha neman lasisi domin hako ma’adanai ko sarrafa su. Sai dai abin takaici, tsawon lokaci gwamnatin ta bari wasu bata-gari, da ba za a ma iya tantance su ba, suke sharbar wannan garabasa ta gurbatacciyar hanya. Da a ce gwamnatin ta mayar da hankali, tabbas da hakan ya zamo mata wata babbar hanyar fadada kudaden shiga, wanda a hannu guda zai bata damar yi wa al’umma aiki da kudaden. Sai dai kash, gwamnatocin baya ba nan suka mayar da hankali ba, handama da babakere ce a gabansu, ba su damu da rayukan talakawa ba ma, balle dukiyoyinsu, ko kuma gina musu kayayyakin more rayuwa.

Shekara daya bayan samu ‘yancin kai a Najeriya, masana sun yi hasashen cewar jahar Zamfara za ta iya zama wani ginshiki na ci gaban tattalin arziki, duba da irin dimbin ma’adanai da Allah ya hore ma. Sun ce za a iya samar da kamfanoni da ma’aikatun sarrafa citta, saka, suga, man kuli, alewa da sauran su, wadanda za su bawa dubban matasa ayyukan yi, har ila yau a janyo hankalin masu zuba hannun jari daga kasashen ketare.

Abun takaici gwamnatocin baya ba su yi tunanin haka ba. Idan da gwamnatocin baya sun so, kudaden da suke karba daga asusun gwamnatin tarayya ya ishe su assasa manyan ayyukan da wata rana gwamnatin jaha za ta dogara da su. Amma da yake ba mutane ne masu kishi ba, haka suka bari lamura na tabarbarewa a hankali har ta kai kowa yana ji a jikinsa.

Sai dai da zuwan sabon Gwamna, Bello Matawallen Maradun, za a iya cewa rana ta fito gari waye. Al’umma jahar Zamfara sun fara ganin haske irin na mulkin dimukradiyya. Abubuwan da suka gagare su tsawon lokacin, Matawallen Maradun ya tashi haikan domin ganin ya magance su.

Babbar matsalar da ta fi ci wa Zamfarawa tuwo a kwarya ita ce tsaro, wanda tuni gwamnan ya fara daukar matakin zazzafan hukunci ga hatta wadanda suke bawa ‘yan bindiga bayanai ko kuma kariya a duk lokacin da suka yi niyyar kaddamar da mummunan shirinsu.

Da alama Gwamnan Zamfara Bello Matawalle da ba wasa ya zo yi ba, domin tare da rakiyar Mataimakinsa Barista Mahadi Aliyu da shugabannin tsaro na jihar, sun shiga dajin dake kusa da garin Wonaka don farauta masu garkuwa da mutanen da suka kai hari kauyen Lilo har suka kashe mutane.

Gwamnan da kansa yake kwanton bauna lokacin da suka hango wani sansanin maharan a cikin daji, cikin tsoro da firgici maharan suka ranta ana kare lokacin da suka ji alamar mutane na tunkaro su. Jami’an  tsaron tawagar gwamnan sun samu nasarar bude wuta har ake kyautata zaton sun samu damar harbin maharan da yawa.

Gwamna Bello Matawalle ya ce bai ga ta zama ba, har sai ya ga bayan maharan dake kashe al’ummar da hakkin kula da rayukansu tare da dukiyoyinsu ke karkashin kulawarsa.

Zan cigaba…

Exit mobile version