Sanata mai wakiltar Zamfara ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Kabir Marafa da Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, sun caccaki gwamnan jihar Zamfara a kokarin shi na daukar matsafa don yaki da tsagerun da suka addabi jihar Zamfaran da kashe-kashe.
Kwamishinan harkokin sarautar gargajiya na jihar Zamfara, Bello Dankande ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, a yayin da aka yi ganawar gaggawa da jami’an tsaro da sarakunan gargajiya da hakiman jihar, ya bayyana cewa gwamnatin jihar na shirin daukar matsafa 1,700 don yaki da barayin da suka addabi jihar.
Amma Sanatocin biyu suna ganin wannan ma maganar banza ce kawai, musamman ganin yadda aka kashe biliyoyin kudade wajen yaki da barayin, amma gwamna Yari sai ya gwammace ya dibu wasu matsafa don yaki da barayin.
Sanata Marafa ya na cewa; sam ban amince da dukkan matakan da gwamna Yari yake dauka ba wajen magance abinda yake faruwa a jihar ta Zamfara, sam gwamnan ba da gaske yake daukar matakan da ya ce yana dauka ba.
‘Na zargi gwamnatin jihar Zamfara da masaniya akan hali da jihar Zamfara take ciki, har yau din nan babu wanda ya fito ya karyata ni, da wasu sun dauka maganata siyasa ce, amma yanzu an fara ankarewa da gaskiyar abinda yake wakana a jihar Zamfara.’ inji Sanata Yari
Shi kuwa Sanata Shehu Sani ya bayyana wannan yunkurin da gwamna Yarin yake na amfani da matsafa a matsayin abun dariya, a cewar shi abunda ke gudana a jihar Zamfara ya nuna gazawar gwamnatin Tarayya da ta jiha wajen samar da tsaro yadda ya dace.
‘Wannan abun kunya ga jihar da take ikirarin bin Shari’a a ce ta koma amfani da tsafi da matsafa wajen kare rayukan al’ummar ta, sannan munafurcin manyan ‘yan siyasar arewa ya kara taimakawa wajen jefa Zamfara din cikin halin da take a yanzu, dauki misali jihar Kaduna inda ita ma take fama da halin rashin tsaro, maimakon a nemu hanyoyin da za a magance al’amarin sai aka mayarda shi rikicin kabilanci da na addini.’ inji Shehu Sani