Zamfara Ta Shirya Wa Kiwo, In Ji Ministan Bunkasa Kiwon Dabbobi
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zamfara Ta Shirya Wa Kiwo, In Ji Ministan Bunkasa Kiwon Dabbobi

bySulaiman
9 months ago
Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya tabbatar wa Ma’aikatar Bunƙasa Kiwon Dabbobi cewa jihar Zamfara na da wuraren da za a yi kiwo.

A ranar Alhamis ne gwamnan ya ziyarci hedikwatar ma’aikatar a wata ziyarar ban girma da ya kai wa ministan, Alhaji Idi Mukhtar Maiha.

  • Hukumar JAMB Ta Zuba Naira Biliyan 6 A Asusun Gwamnatin Tarayya A Shekarar 2024
  • Da Ɗumi-Ɗumi: Babban Layin Wutar Lantarkin Nijeriya Ya Lalace Karon Farko A 2025

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa, jihar Zamfara, kasancewarta jihar noma da kiwo tana taka rawar gani a aikin ma’aikatar binƙasa kiwon dabbobi.

Sanarwar ta ƙara da cewa, an ƙirƙiro ma’aikatar ne a watan Yulin 2024 domin gyara masana’antar kiwon dabbobin Nijeriya, da samar da yanayi mai inganci, da ƙarfafa zuba jari na cikin gida da na ƙasashen waje, da kuma inganta samar da abinci.

A yayin ziyarar, Gwamna Lawal ya bayyana aniyar gwamnatinsa na haɗa kai wajen lalubo baiwar da jihar Zamfara ke da shi.

“Minista, kamar yadda ka sani, Zamfara al’umma ce ta noma. Shi ya sa taken mu shi ne, ‘Noma Abin Alfaharinmu Ne’.

“Mun zo nan ne a yau domin taya ku murna da kafa wannan sabuwar ma’aikatar, wadda nake da yaƙinin ta dace. Bugu da ƙari, muna da burin samar da haɗin gwiwa mai ƙarfi tsakanin jihar mu da ma’aikatar.

“A Zamfara, madatsun ruwa da dama a faɗin jihar na buƙatar gyara don samar wa dabbobi da ruwa, haka kuma za a iya samun damar ɗaukar duk wani shiri.

“Muna gayyatar Minista da tawagarsa da su ziyarci Zamfara domin duba yanayin kiwo na jihar.”

A lokacin da yake mayar da martani, ministan harkokin kiwo, Idi Mukhtar Maiha, ya gode wa gwamna Lawal bisa ziyarar da ya kai ma’aikatar.

“Tun da aka kafa ma’aikatar, ba mu samu ziyarar wani gwamna mai zartarwa da ke da buƙatar jin abin da za mu iya bayarwa ba.

“Ina so in tabbatar muku cewa a shirye muke mu ba ku haɗin kai don kawo sauyi da magance matsalolin ku a fannin kiwon dabbobi a Zamfara.

“Bangaren kiwo ya daɗe yana aiki ba bisa ƙa’ida ba. Za mu zamanantar da wannan fanni ta hanyar tsare-tsare daban-daban.

“Gwamna, jihar Zamfara ce za ta zama jihar da za ta yi gwaji domin nuna ajandar sabuwar ma’aikatar. Da wannan haɗin gwiwa za mu mayar da Gidan Jaji da ke Zamfara wata ƙaramar cibiyar kiwo,” inji ministan.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung
Manyan Labarai

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio
Manyan Labarai

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo
Manyan Labarai

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025
Next Post
Rahoto Ya Nuna Yadda Kanana Da Matsakaitan Kamfanonin Sin Ke Tafiya Cikin Tagomashi

Rahoto Ya Nuna Yadda Kanana Da Matsakaitan Kamfanonin Sin Ke Tafiya Cikin Tagomashi

LABARAI MASU NASABA

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version