Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Kungiyar Kwadago ta ƙasa reshen jihar Katsina ta yi barazanar ɗauki mataki akan kamfanin mulmula ƙarafa na Dana da ke Katsina saboda rashin kyautatawa ma’aikata da rashin samar da yanayin aikin mai kyau.
Shugaban kungiya kwadago a jihar Katsina, kwamred Tanimu Saulawa ya bayyana haka a wata ziyarar ‘yan uwantaka da kungiyar ta kaiwa ma’aikatan kamfanin mulmula karafa na Dana da ke Katsina
Ya kuma bayyana cewa kungiyar kwadago ta damu ainun saboda yadda ta tarar da yanayin aiki a waje, sannan ya ƙara da cewa an hana ma’aikata haƙƙinsu da yakamata aba su, amma kawai an maida su ma’aikatan wucin gadi karfi da ya ji, kuma gahsi babu wani albashi mai tsoka.
Da yake magana a madadin shuwagabanin kamfanin mulmula karafe na Dana, Sanjeeb Dash ya bayyaba cewa kamfanin bai daɗe da dawowa akan aikin ba, yanzu sati biyu kenan da suka dawo aiki.
Ya kuma bada bada tabbacin kafin kungiyar kwadago ta sake dawo kawo wata ziyara za su tara an yi duk abinda ya kamata na kyautatawa ma’aikatan mulmula karafa na Dana da ke katsina.
Idan a za a iya tunawa an sanar da kamfanin mulmula karafa ne da gwamnatin tarayya ta yi a shekarar 2006 a ƙarƙashin tsarin nan na sayar da ƙadarori mallakar gwamnati a wannan lokaci.