Connect with us

SIYASA

Zamu Bunkasa Mazabar Hadeja/Auyo/Kafin Hausa —Dan Takara A PDP

Published

on

BARISTA BELLO UMAR HADEJA dan takarar Majalisar Wakilai ne ta tarayya a karkashin inuwar jamiyyar sa ta PDP, a zaben 2019, inda yake son ya wakilci alumarsa ta mazabar Hadeja/Auyo/Kafin Hausa. A hirarsa da ABUBAKAR ABBA a Kaduna, ya bayyana dalilan da yasa ya fito takarar. Ga yadda hirar ta kasance.
Me ya baka sha’awar shiga siyasa?
Ni a siyasa aka haifeni. Tun da na tashi na samu mahaifina yana siyasa. Amma a yanzu dai halin da mutanen mazabata suke ciki, shine ya sa ni na shiga harkar neman takara. Saboda ina ganin ina da wata gudunmawar da zan iya bayarwa wadda sauran ‘yan takarar da kuma wanda yake kan kujerar yanzu bazasu iya bayarwa ba.

Tun yaushe ka fara yin siyasa?
Tun 2003 nake cikin harkarkar a Kasar Hadejia. Tun daga manna fasta har na zo ake yin shawarwari da ni ake damawa da ni a wurin ‘yan takara. Kawai dai ban taba neman takarar kujerar siyasa ba ko ta shugabanci sai yanzu.

Idan alummar mazabar ka suka zabe ka, wadanne irin kudurori zaka gabatar a gaban majalisa don kawo masu ci gaba da kuma yan Najeriya baki daya?
Tunda ake aika ‘yan majalisar tarayya da aka dawo da demokradiyya mu a mazabar mu, bamu taba samun wakilin da ya je ya wakilcemu ba yadda ya kamata. Kafin na yi maganar kudiri uri, idan ka dauki maganar yin magana a majalisa ko wurin bada gudunmawar bayani idan ana zauren majalisa mu wakilinmu baya iya fitow ya yi magana ko wurin yarda da kuduri ko cewa baya goyon baya. Sannan babu kuduri , babu ayyukan mazaba da wakili zai kawo wa yankinsa. Ko kuma idan ka dauki maganar zuwa yin kamun kafa ga wani Minista ko wani babba a hukumomin gwamnatin tarayya wajen nemowa yankinsa aikin Gwamnatin Tarayya ga yankinsa kamar yadda ko wane dan majalisa ya kamata ya yi, mu bamu samu wannan damar ba.

A ina ne kaga wanda yake a kan kujerar a yanzu kaga ya gaza kake son ka fafata dashi a zaben?
Shi wannan wanda kake nufi yana da matsaloli da yawa na harkar tafiyarda aiki irin na majalisa. Kaga dan majalisa yana da bukatar zurfin ilimin boko, sanin mutanen sauran jihohi da yankuna da kuma addinai da yare a Najeriya. Bayan haka, sanin doka da yadda ake yinta suna daga cikin abinda mutum yake bukata. Wannan mutum wai mai shedar karatun malanta na biyu tun daga shekarar 1985 da ya samo daga Kwalejin horas da Malamai dake a jihar Kano, amma abin bakincike shine, idan ka tsare shi ba zai iya fada maka me yakeso ya yi alummar mazabar mu ba. Har fata nake matasa su hada muhawara a kafin zabe a tsakanin na dashi don mu fafata. A nan mutane zasu gane me suka rasa da suka aika wannan bawan Allah 2015.

A matsayin ka na matashi, wanne babban shiri na musamman zaka yiwa matasan mazabar ka in ka lashe zaben?
Takarata dama tasu ce, domin sun gama makaranta, wasu dashedar kammala karatu ta Difiloma zuwa Digiri, kai wasu ma har babban Digiri, amma babu aikin yi kuma babu wata sana’a da zasu iya yi da zata kawo musu aikin yi. Idan ka zo zaka ga bamu da wasu kamfanoni da suke bada aikin yi ga matasa, babu wani aiki na cigaba da gwamantin tarayya ta kawo mana, kuma abin ya yi wa gwamnatin jiha yawa. Dole ne na samo wa matasa abin yi, dole na taimakawa masu su je makaranta su koyo mana sana’o’i da kimiyya da kuma ilimin boko wanda zai taimaka mana wajen gina yankinmu ba tare da ya bata tarbiyyarmu ta addininmu ko gargajiya ba.

Yaya kaga karbuwar PDP ga alummar dake mazabar ka?
Mu dama a Jigawa ba PDP ce mutane basa so ba domin ta yi rawar gani a jihar a lokacin mulkin tsohon Gwamna Sule Lamido, don any titin da hada duka kananan hukumomi 27 titi mai kyau mai inganci, wanda har yanzu shi muke takawa. An kawo cibiyoyin ilimi na tarayya , an kawo ma’aikatu na gwamnatin tarayya aka kuma taimaka a kowa wanne fanni na cigaban al’ummar Jigawa. Zaben 2015 da muka rasa gwamnatin Jigawa bada sonmu bane. Saboda guguwar Buhari ce da kuma matsalar tsaro ta Boko Haram a kasa baki daya da ta kwaso wasu irin mutane suka zo suka samu shugabanci da wakilcin jama’a. Har yanzu kuma mutanen Jigawa suna tare da PDP kuma ina da yakinin idan muka tsayar da mutane nagartattu wadanda zasu iya yi wa mutane aiki, za a sake zabarmu saboda yanzu mutane sun gane, baza su sake yin kuskuren zaben “SAK” ba kamar yadda aka yaudaresu a baya suka yi zaben tumun dare ba.
Mutanen mazabata sun nuna min halarci sosai. Tun da na fito maganar neman takara ake nuna min halacci ake nunamin kauna. Kuma na san ba wai ni din bane kadai, har da jam’iyyata ta PDP.

Wanne kira za kayi ga alummar mazabar ka musamman don su kara baka goyon baya a lokacin zaben?
Ina so al’ummar su duba wanda ya fi cancanta, wanda ya goge, ya san mutane, ya san doka kuma ya san mutuncin manya da matasa, wanda zai kawo masu da kuma ci gaban mazabar.Kada mu yarda da wanda muka gwadashi ya yaudare mu, kada mu yarda da wanda zai zo ya bamu kudi ya yi tafiyarsa sai shekara -shekara ya zo ya mana ciko da yashi idan ruwa ya mana barna. Kar mu yarda a cucemu. Ina kira ga mutanen mu fito kwanmu da kwarkwata mu yi zaben 2019. Kuma dai zan so a ce an min ruwan kuri’a in sha Allah.

Daya daga cikin gwanayen ka musamman tsohon Gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido yana neman shugaban kasa, wanne irin goyon baya zaka samar masa a lokacin zaben?
Baba Lamido babana ne kuma shugabana ne. Bana mantawa, mun zauna da shi yake cemin “Bello idan mutum ya ce ka zabe shi, sai kace masa ya baka hujja”, toh ni bisa hujja nake goyon bayansa. Aikin da ya yi a shekaru takwas a Jigawa ba gwamnoni da yawa bane zasu tarar da jiha kamar yadda ya samu Jigawa kuma ya canja ta ba kamar yadda ya yi. Aikinsa ya taba kowace karamar hukumar jihar kuma ya taba kowace masarauta, ya taba kowane irin mutum ntun daga mai lafiya har nakasasshe, mai arziki da talaka, babba da yaro, dan kasuwa da ma’aikacin gwamnati a jihar. Mu dai babu abinda zamu ce masa sai godiya kuma da fatan alkhairi.

Yanzu neman takara kake a PDP, da me kake tunannin ka fi sauran ‘yan takarar na PDP?
Wato ina ganin a cikinmu ‘yan takarar da muke neman a bamu damar tsayawa zabe ina ganin na fi sauran gogewa wajen sanin mutane a kasarnan, kamfanoni da zasu kawo cigaba a yankin mu, sanin doka da yinta, mu’amala da mutanen yankin mu ta yadda zasu iya fadamin matsalolinsu kuma na yi kokarin magancewa, kuma ni matashi ne da jinni a jikina babu alamar gajiyawa. Bana tinanin akwai wanda ya tara duka wadannan abubuwan a cikinsu.

Kana ganin jam’iyyarku za ta baka takarar?
Tabbas ina da yakinin hakan, zata yi min adalci ta bani takara. Ya kamata a ce an wuce maganar wani maganar daga wacce shiyya mutum ya fito. Idan kuwa aka yi kokarin haka toh dole ne mu kai kukanmu wurin jagoranmu Sule Lamido, na san zai sharemana kukanmu. Yanzu abinda muke bukata a PDP shi ne mu tsayar da mutum nagartacce wanda mutane suke kauna kuma zasu zabe shi a matsayin dan majalisarsu.
Bisa wadannan dalilan nake ganin za a yi adalci kuma ina ganin da alamun da nake gani, zan samu takara idan dai jam’iyya ta tsaya ta yi adalci.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: