Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya sha alwashin cewa ba za su amince da tozarta maniyatan jihar Katsina ba saboda haka duk jami’in da aka kawo rahotan ya ci mutunci wani Alhaji za su dauki mataki a kansa.
Masari ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke jawabin bankwana ga maniyata da suka fito daga jihar Katsina inda ake sa ran kimanin maniyata 4930 ne za su sauke farali a wannan shekarar.
Gwamnan wanda mataimakinsa Alh. Mannir Yakubu ya wakilta ya ce aikin hajji, aikin ne da ya ke bukutar ilimin yin sa kafin mutum ya aikata shi wanda hakan ya sa gwamnatin jiha ta dauki nauyin taron bita ga maniyata a fadin jihar.
Alh. Mannir Yakubu ya ce tsarin nan na jirgin da ya kaika shi zai dawo da kai yana nan saboda haka ya yi kira ga maniyatan da su girmama wanna tsari domin samun nasarar da ake bukuta.
A na shi jawabin, shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar Katsina Muhammad Abu Rimi ya ce, duk abinda suke bukutar na tafiyar da wannan aikin na bana gwamnatin jihar Katsina ta riga ta ba su, abinda kawai ya rage shi ne a samun hadin kai maniyata daga jihar Katsina.
Idan za a iya tunawa jihar Katsina ita ce jiha wanda ta biya kudin kujera mafi karanci a fadin kasar nan, kuma hukumomin sun bayyana cewa fiye da kashin 80 na maniyatan bana manoma ne.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahotan akalla maniyata daga jihar Katsina kimanin mahajata 481 suka tashi a jirgin farko a ya yin da 539 suka tashi a jirgi na biyu zuwa garin Madina.