Zamu Doke Manchester City A Jamus – Haaland

Haaland

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund, Erling Braut Haaland ya bayyana cewa suna da karfin da zasu doke kungiyar kwallon kafa ta Manchester City a wasan da zasu fafata a sati mai zuwa.
Tauraruwar dan wasan Borussia Dortmund Erling Braut Haaland na ci gaba da haskawa ya yinda farin jininsa ke ci gaba da kaure Duniyar kwallo ba kadai ga ‘yan kallo ba har tsakanin ‘yan wasa da kuma akalan wasan.
Sai dai matakin alkalin wasa Obidiu Hategan na neman Braut Haaland ya yi masa sa hannu, ya janyo cece-kuce da ya kai ga tafka muhawara akai wanda kociyan Manchester City, Pep Guardiola ya bayyana cewa alkalin wasan yayi daidai kuma yana da damar yin hakan.
Bayan kammala wasan na ranar Talata wanda Dortmund ta sha kaye da kwallaye biyu da daya dai anga yadda Hategan ya nufi Haaland tare da mika masa katina biyu don ya yi masa sa hannunsa, wanda ke nuna shi magoyi bayansa ne.
Tuni dai Hategan ya fara fuskantar caccaka daga masu sharhi wasanni, inda Owen Hargreabes tsohon dan wasan Manchester City ke ganin bai kamata alkalin wasan ya yi hakan a gaban sauran ‘yan wasa ba.
Sai dai Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola da ke fatan sayo Haaland a sabuwar kaka, ya ce da yiwuwar alkalin wasan ya nemi sa hannun ne saboda ‘ya’yansa magoya bayan Haaland.
Sai dai har yanzu alkalin wasan bai ce komai ba akan lamarin wanda yake neman zame masa alakakai ganin cewa shi alkalin wasa ne kuma kowanne dan wasa nasane kamar yadda yake a doka.

Exit mobile version