Shugaban Hafsan Sojojin Nijeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ya bayyana cewa; rundunar Sojin Nijeriya ta amince da samar da Barikin kwararrun Soji wanda za a gina a garin Okenen jihar Kogi.
Buratai ya bayyana hakan ne a jiya Juma’a a garin Okene a yayin da bikin bude wurin da za a samar da sabon Barikin Sojin a karamar hukumar Okene a jihar Kogi.
Manjo Janar Ademo Salihu, Kwamandan sashen horasawa da ba da umurni wato TRADOCI a takaice reshen Minna, shi ne ya wakilci Buratai din, inda ya tabbatar da cewa; sabon Barikin kwararrun Sojin da za a samar zai bunkasa bangaren sha’anin tsaro tare da kare rayukan al’umma a jihar Kogi.
Ya ce; sun zabi su yi Barikin a jihar Kogi ne ganin yadda jihar ta zama mashiga tsakanin Arewacin Nijeriya da Kudancin Nijeriya. Ya ce; shiyasa gwamnatin tarayya ta zabi ta yi Barikin a wurin domin kare rayukan al’ummar yankin da ma kasa baki daya.