Abba Ibrahim Wada" />

Zamu Mu Iya Sake Lashe Kofin Zakarun Turai Bana – Lewandowski

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen, Robert Lewandowski, ya bayyana cewa kungiyar tasa zata iya sake lashe gasar cin kofin zakarun turai karo na biyu a jere idan suka sake dagewa.

Mai rike da kofin Zakarun Turai, Bayern Munich ta doke kungiyar kwallon kafa ta Lazio da ci 4-1 har gida a wasan zagaye na biyu a Champions League ranar Laraba duk da cewa tun farko anyi hasashen zakarun duniyar sune zasu samu nasara.
Jamal Musiala ya zama matashin dan wasan Ingila da ya zura kwallo a raga a gasar kofin zakarun turai na Champions League a karawar da suka yi a babban birnin kasar Italiya wato Rome.
Matashin dan wasan mai shekara 17 da haihuwa kuma shi ne mai karancin shekaru a kungiyar ta Jamus da ya ci kwallo a gasar ta zakarun Turai a tarihi wanda hakan yasa ya kafa sabon tarihi a kungiyar wadda ata lashe gasara a kakar data gabata.
Robert Lewandowski ne ya fara cin kwallo kuma kwallo ta 72 da ya zura a raga a gasar, ya zama dan wasa na uku a jerin wadanda suka fi cin kwallaye a gasar kuma hakan yana nufin ya haura tsohon dan wasan Real Madrid  Raul kenan.
dan wasa Leroy Sane ne ya ci kwallo ta uku sannan ya sa Lazio ta ci gida daga baya kungiyar ta Italiya ta zare daya ta hannun Joakuin Correa kuma a hakan aka tasi daga fafatawar kafin kuma a buga zagaye na biyu.
Bayern Munich wadda ta lashe kofuna guda shida a watanni tara baya ta barar da maki a gasar Bundesliga, tun bayan da ta lashe Club Wold Cup sannan kwallon da Lewandowski ya ci ta zama ta uku a cin kwallaye a Champions League, bayan Cristiano Ronaldo mai guda 134 da kuma Lionel Messi mai guda 119 a raga.
Matashin dan kwallon Ingila da ya zura kwallo a raga a Champions League a tarihi a baya shi ne Aled Odlade-Chamberlain – wanda ya ci wa Arsenal kwallo a karawa da kungiyar kwallon kafa ta Olympiakos kuma ya yi wannan bajintar cikin watan Satumba na shekarar 2011 a lokacin yana da shekara 18 da kwana 44 a duniya.
Wannan ne karon farko da Lazio ta kai wasan zagaye na biyu a Champions League tun bayan shekara 21 sai dai nan gaba Bayern Munich za ta karbi bakuncin Lazio a wasa na biyu ranar 17 ga watan Maris.

Exit mobile version