Connect with us

WASANNI

Zamu Yi Kokarin Lashe Kofi A Wannan Kakar

Published

on

Mai koyar da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Julian Lepatugui ya bayyana cewa zasuyi iya kokarinsu don ganin sun lashe kofi a wannan shekarar duk da ganin da akewa kungiyar na ganin cewa bazasuyi wani abu ba.
Real Madrid dai har yanzu a kasuwa take wajen neman dan wasan da zai maye mata gurbin Cristiano Ronaldo wanda yabar kungiyar zuwa Jubentus a kakar wasannan kuma tuni aka fara ganin rashin dan wasan zai bawa kungiyar matsala.
Kungiyar dai tasha kashi a hannun abokiyar hamayyarta wato Atletico Madrid a wasan karshe na cin kofin Super Cup da suka fafata a satin daya gabata hakan yasa aka fara ganin rashin Ronaldo ko kuma rashin siyo wani babban dan wasa zai bawa kungiyar matsala.
Sai dai tuni kociyan kungiyar ya bayyana cewa rashin Ronaldo bazai basu matsala ba tunda akwai kwararrun ‘yan wasa a kungiyar sannan kuma ga matasan ‘yan wasa irinsu Asensio da Binicios wadanda zasu haska anan gaba.
Yaci gaba da cewa yanason kungiyar ta siyo babban dan kwallo wanda zai maye gurbin Ronaldo amma kuma idan kungiyar bata samu ba yana farin ciki da ‘yan wasan da suke kungiyar a yanzu haka kuma a shirye yake dayayi aiki tare dasu.
Real Madrid dai ta nemi dan wasa Edin Hazard daga kungiyar Chelsea sai dai Chelsea tace dan wasan nata bana siyarwa bane kuma shima dan wasan da kansa ya bayyana cewa zaici gaba da zama a kungiyar har zuwa kakar wasa mai zuwa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: