Abba Ibrahim Wada" />

Zan Cigaba Da Amfani Da Matasan ‘Yan Wasa —Emery

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Unai Emery, ya bayyana cewa zai cigaba da amfani da matasan ‘yan wasan da kungiyar take dasu a halin yanzu domin gina kungiyar da matasan ‘yan wasa wadanda zasu kai kungiyar ga nasara.

kwalaye daga ‘yan wasan da ba a dade da yayewa daga tawagar matasa ta Arsenal ba, wato Joe Willock da Bukayo Saka sun taimaka wa Arsenal din a wasa mai sarkakiya da ta fafata da Eintracht Frankfurt a gasar zakarun Turai ta Europa a daren Alhamis, lamarin da ya sa ta fara gasar ta wannan kaka da kafar dama.

Willock ya ci wa Arsenal kwallon ta ta farko a wasan sakamakon kwallon da ta daki jikin dan wasan Frankfurt, kafin Saka ya saka kwallo ta biyu a minti na 85 na wasan wanda Arsenal din taje har kasar Jamus.

Minti biyu bayan wannan kwallo, dan wasan gaba Pierre-Emerick Aubameyang ya kara ta uku, lamarin da ya kawo karshen rashin nasara da dasaura kiris ta jera wasanni uku tana yi a kakar wasa ta bana.

Arsenal ta samu karin damammaki amma ita ma din sai da mai tsaron ragarta Emiliano Martinez ya rufa mata asiri saboda ‘yan wasan bayanta sun yi bacci saboda mai tsaron ragar dan kasar Argentina ya hana kwallayen Filip Kostic and Andre Silba shiga raga a zubin farko na wasan.

Sai dai bayan an tashi daga fafatawar kociyan na Arsenal, Unai Emery, ya bayyana cewa matasan ‘yan wasan kungiyar daya bawa dama sunyi amfani da damar da suka samu saboda haka zai cigabada basu damarmaki anan gaba.

Exit mobile version