Zan Cigaba Da Zura Kwallaye – Ibrahimovic  

Kwallaye

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta AC Milan, Zlatan Ibrahimovic, ya bayyana cewa yanzu ya fara zura kwallo a raga kuma yana fatan nan gaba kadan zai kafa tarihin wanda yafi kowa zura kwallo a kungiyar AC Milan.

Zlatan Ibrahimovic ya kafa tarihin cin kwallaye 500, ya yin karawar da AC Milan ta doke kungiyar kwallon kafa ta Croton da ci 4-0 ta kuma kasance a saman teburin gasar seria A ta Italiya da maki 49.

AC Milan ta koma baya da maki biyu a gaban abokiyar hamayyarta Inter Milan wacce ta yi sama bayan nasarar da ta doke Fiorentina da ci 2-0 a ranar Juma’a, yayin da ta baiwa Jubentus dake rike da kambun gasar ta Seria A tazarar maki biyar a matsayi na uku, bayan doke Roma da ci daya mai ban haushi a ranar Asabar.

A halin yanzu adadin kwallayen da Ibrahimovic ya ci a kungiyoyin da ya haskawa da kuma kasar sa ta Sweden sun kai 501 duk da cewa wasu suna ganin a cikin kwallayen babu wadanda ya zura  kasarsa ta haihuwa Sweden

“Ina fatan ci gaba da zura kwallaye saboda aikina ne cin kwallo duk da cewa shekaru suna ci gaba da yawa a kaina sai dai ina kokarin ganin na gyara jikina domin kasancewa cikin gwarazan ‘yan wasa a duniya” in ji Ibrahimovic

Ibrahimovic dai ya buga wasanni a manyan kungiyoyi da dama da suka hada da kungiyar kwallon kafa ta Ajad ta kasar Holland da Jubentus da Inter Milan da Barcelona da PSG da Manchester United da kuma kungiyar AC Milan daya buga wasa har karo biyu.

Exit mobile version