Zan Dau Mataki Kan Duk Basaraken Da Aka Samu Da Hada Kai Da ‘Yan Ta’adda –Sarkin Ningi

Daga Khalid Idris Doya,

Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya, ya gargadi hakimai, dakatai da sauran masu rike da sarautun gargajiya da suke karkashin masarautarsa da cewa su tsame kansu daga dafawa ko baiwa ‘yan ta’adda mafaka a yankunansu, yana mai cewa duk wani basaraken da ya samu da hannu wajen hada kai da ‘yan ta’adda zai rasa rawaninsa.

Sarkin wanda ke wannan gargadin a yayin wani taron gaggawa da ya kira inda ya tara dukkanin masu rike da sauratun gargaji da suke karkashin ikonsa domin tattauna batutuwan da suka shafi tsaron masarautar.

Yana mai cewa shi a kashin kansa baya wasa ko kadan da sha’anin tsaro don haka ne ya nemi masu sarautun da su kara himma da kokari wajen kare yankunan da suke mulka domin tabbatar da tsaro da kare rayukan al’umma.

Ya ce: “Na kira taron gaggawa domin ganawa da sarakunan da suke karkashin wannan masarautar ne kan wani rahoton da muka gani wanda kafafen watsa labarai suka yada kan cewa ana zargin sarakunan wannan yankin da hada baki da ‘yan ta’adda. Wannan dalilin ya sanya na kirasu domin na musu kashedi don ko kadan rahotonnin ba su min dadi ba.

“Na tara sarakuna nawa na tambayesu menene gaskiyar labarin da na ji, kuma mun kaddamar da bincike duk wanda muka samu hannu ‘in akwai’ zai fuskanci fushinmu, amma ina tsammanin ma babu wani basaraken da ke hada baki da ‘yan ta’adda a masarautata.

“Amma fa in akwai, domin muna nan muka kan gudanar da bincike, za mu kori kowaye idan muka samu na hada baki da ‘yan ta’adda don ba za mu lamunci hakan ba ko kadan,” sarkin ya bayyana.

Alhaji Danyaya ya kuma bayyana cewar gwamnatin jihar karkashin Sanata Bala Muhammad tana kokarin bunkasa zaman lafiya da tsaro, don haka ne ya bayyana cewar su a matsayinsu na sarakuna suna kara bada goyon baya da gudunmawa domin tabbatar da inganci tsaro a jihar.

A zama da sarakunan da sarkin ya kira a fadarsa na tsawon awanni uku, ya samu halartar dukkanin hakimai, dakatai da masu unguwannin da suke karkashin masarautar inda dukkaninsu suka yi wa sarkin bayanin halin tsaro da yankunansu ke ciki domin daukan matakan da suka dace.

Wakilinmu ya labarto cewa sarakunan da suke yankin sun bayyana cewar basu da alaka da ‘yan ta’adda, sai dai sarkin ya nanata ya kuma jaddada musu cewar dukkanin mai niyyar bada goyon baya wa ‘yan ta’adda ya gaggauta sauya tunaninsa domin ba za su taba barin hakan ya faru a karkashin masarautarsa ba.

Muhammad Danyaya ya kuma jawo hankalin sarakunan a kowani lokaci suke rokon addu’o’in malamai da al’ummar yankunansu domin tabbatuwar zaman lafiya da tsaro a masarautar Ningi da jihar Bauchi tare da kasa baki daya.

Ya kuma tabbatar da cewa daga yanzu kunnuwarsa a bude suke dukkanin wani basaraken da ya samu da hannu wajen mara wa ‘yan ta’adda baya tabbas zai fuskanci mummunar hukunci da zai iya kaisa ga rasa rawaninsa.

Exit mobile version