Muhammad Awwal Umar" />

Zan Dinke Barakar Da Ke Tsakanin ‘Yayan Jam’iyyar APC Da Hadin Kan Su- Garkuwa

Mataimakin shugaban jam’iyyar APC ta jiha mai wakiltar yankin Neja ta arewa, Hon. Aminu Musa Bobi ( Garkuwan Bobi) ya sha alwashin dunke barakar da ke damun jam’iyyar a yankin da yake shugabanta a Neja.

Garkuwan ya bayyana hakan ne a lokacin zamansa da masu shugabannin jam’iyyar na yankin da kananan hukumomin da ya samu damar ziyarta a karshen makon nan. Mataimakin shugaban jam’iyyar yace dukkanin tafiyar da aka faro sai ta samu irin wannan turjiyar, hanya mafi saukin magance shi sune hakuri da hada kai dan yin aiki tare.

“Tafiyar da na faro yanzu ta kowa da kowa ce, shi yasa ba tare da bambamci ba, ni ke bin duk wani jigo a jam’iyyar nan dan neman hadin kai da goyon baya ta yadda zamu hada hannu mu magance duk wasu kurakuran da mu ka yiwa juna dan cigaban jam’iyyar mu. Tabbas, an yi ma wasu ba daidai a baya musamman yadda aka sanya son zuciya aka ci zarafin wasu a tafiyar APC, da yardar Allah da goyon bayan ku, da hadin kan ku APC za ta dawo da numfashinta kan tafiya ta gaskiya yadda kowa zai anfana.”

Tunda farko dai, mataimakin shugaban jam’iyyar ya bada tabbacin cewar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a matakin tarayya da ta Alhaji Abubakar Sani Bello a matakin jiha sun zo da kudurce kudurcen za su anfani al’ummar kasa da jihar, amma rashin samun wakilai da zasu rike al’umma kamar yadda manufar jam’iyyar ta ke a siyasance shi ya kai jam’iyyar a wannan halin da ta ke ciki a yau.

Manufofin da shugaban jam’iyyar ta kasa, Gwamna Mai Mala Boni na jihar Yobe, da mataimakinsa a yankin arewa ta tsakiya, Gwamna Alhaji Abubakar Sani Bello suke akai shi ne na dawo da martabar jam’iyyar da hada hannu da ‘yan kasa wajen kawo cigaba masu alfanu. ” Ina kira da babban murya ga duk wanda aka yiwa ba daidai a tafiyar shugabancin na baya, da ya hakura ya dawo mu kafa harsashi na gaskiya ta yadda al’umma zasu anfani mulkin dimukuradiyya.

Da yardar Allah da goyon bayan ku, duk wasu matsalolin da muke fuskanta a jam’iyyar nan za mu magance shi, saboda haka goyon bayan ku a wannan tafiyar tana da muhimmanci a tafiyar siyasar APC.

Mataimakin shugaban jam’iyyar dai zuwa yanzu zai cigaba da yin rangadi a dukkanin kananan hukumomi takwas na yankin Neja ta arewa dan ganawa da shugabannin jam’iyyar APC daga matakin mazaba zuwa kananan hukumomi da shugabannin shiyya na jam’iyyar da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a yankin dan walwale matsalolin da ta ke samu tsakanin ‘yayanta.

Exit mobile version