Connect with us

WASANNI

Zan Iya Barin Manchester United Nan Gaba Kadan

Published

on

Dan wasan Faransa da ke buga wasa a kungiyar Manchester United, Paul Pogba, ya ce baya tsammanin sauya sheka ko da a kakar cinikayyar ‘yan wasa ta watan Janairu bayan takun sakar da ya ke fuskanta tsakaninsa da kociyan kungiyar Jose Mourinho.
Kalaman na Pogba dai na zuwa ne a dai dai lokacin da wasu jita-jitar maye gurbin Mourinho da Zinadine Zidane ke ci gaba da ruruwa, wanda dan wasan ya ce zai fi kowa farin ciki da hakan.
Pogba wanda shi ne dan wasan manchester United mafi tsada data siya kan Yuro miliyan 89 daga Jubentus har yanzu sun gaza sasantawa da Mourinho amma duk da haka ya ce bai ga yiwuwar sauya shekarsa nan kwana kusa ba.
Pogba mai shekaru 25 wanda ya lashe kofin duniya bana, akwai dai rade-radin da ke cewa ya na kokarin komawa Barcelona ko da dai ya musanta hakan, yayinda a bangare guda itama manchester United din ta ki amincewa da tayin na Barcelona a kakar musayar ‘yan wasan da ta gabata.
“Ban san abin da zai faruba nan da wasu ‘yan watanni ba amma makoma ta tana hannun Manchester United saboda haka sai dai mu tsaya muga yadda abubuwa za su kasance” in ji Pogba.
Pogba dai kawo yanzu ya zura kwallaye biyu cikin wasanni hudu daya bugawa kungiyar a gasar firimiya kuma a wasa na farko dana biyu a gasar firimiya shine yafito a matsayin kyaftin din kungiyar.
Advertisement

labarai